LabaraiBidiyo: Bayan ba su sadaka, matashi ya ritsa makafi...

Bidiyo: Bayan ba su sadaka, matashi ya ritsa makafi 2 su na latsa wayoyinsu a cike da nishadi

-

- Advertisment -spot_img

Wani dan Najeriya ya sha mamaki bayan kama wasu makafi biyu su na latsa wayoyinsu mintina kadan da ba su sadaka, LIB ta ruwaito.

Dama tun farko ya gansu ne zaune a titi su na bara inda yayi tunanin makafin gaske ne, hakan yasa ya basu kudi a matsayin sadaka.

Daga bisani kuma sai ya gansu su na latsa wayoyinsu. Wannan lamarin yasa ya dauki wayarsa ya hau yi musu bidiyo inda ya wallafa wa jama’a a kafafen sada zumuntar zamani don su hankalta.

Ga bidiyon a kasa:

Yadda na ritsa mijina yana lalata da mata 8 akan gadon aurenmu, Matar aure

Wata mata wacce muryarta ta dinga yawo a kafar sada zumuntar zamani ta TikTok a kwanakin baya inda ‘yan mata su ka dinga hawa muryarta ta bayyana yadda ta ritsa mijinta da mata 8 akan gadon aurensu.

Kamar yadda bidiyon wanda shafin lucky Udu ya wallafa a Facebook, an ji yadda matar take bayani dalla-dalla inda tace an samu wannan muryar tata ne a jawabin da tayi a kotu.

A cewarta, mijin nata baya aikin fari balle baki, sai shaye-shaye da bin mata, amma a wannan karon abinya ta’azzara don ta dawo daga tallar magungunar kwari ne ta ritsa shi da mata 8.

A cewarta, shigarta dakin ke da wuta ta ji sautinsa da na matan, sai ta karasa ciki taji yana canja matan yayin da ya ke lalata da dukansu kamar yana canja zannuwa.

A cewarta, mamaki ne ya kama ta hakan yasa ta nemi jin wannan ba’asin, sai ya gaura mata mari tare da ce mata kada ta dinga shiga harkokin da basu shafe ta.

Ta bayyana yadda ta tattara ya nata ya nata ta tafi gidan iyayenta tare da yaranta biyu wadanda dama ita ce take kulawa da su.

Sai daga bisani ta amsa gayyatar kotu inda alkali ta nemi jin ta bakinta bayan mijin ya kai kararta wanda ta shaida cewa mata 8 ta kama shi da su.

Anan ne alkalin ta nemi su shirya amma duk da haka abin ya ci tura. Ta ce yanzu haka ba sa tare kuma tana ci gaba da lallaba rayuwarta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you