34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Wawaye ne ke auren soyayya, saboda kudi zan yi aure, Cewar amarya Habiba

LabaraiWawaye ne ke auren soyayya, saboda kudi zan yi aure, Cewar amarya Habiba

Wata amarya mai suna Habiba Gado ta wallafa hotunanta a Facebook na kafin aurensu ne tare da angonta wanda taken da ta yi wa hotunan ya yi matukar daukar hankulan mutane da dama.

Aure saboda kudi zan yi, babu abinda ya dame ni da shirmenku, a cewarta.

Ta kara da cewa “Wawaye ne ke auren soyayya.”

Ga wallafar tata:

her post
Wawaye ne ke auren soyayya, ni auren kudi zan yi, Cewar amarya Habiba

Ba dai a tabbatar ko wasa take yi ba ko kuma da gaske take kuma har yanzu har yanzu bata bi bayan wallafar tara yi wata wallafar wacce za ta wanke waccan ba duk da fiye da mutane 2,000 sun yi ta tsokaci.

Shi kuma angon nata ya wallafa bidiyonsu tare na hotunan kafin aurensu inda shi ma yace, “Wawaye ne ke auren soyayya 2022.

Angon mai suna Djbenzee Junior ma ya wallafa:

Mutumin da ya samu mata ya samu abu mai tsada kuma Ubangiji ya yi masa babbar kyauta. Ni dai na samu tawa shi ne nace bari in sanar muku.”

Ga wallafar ta shi:

his post
Wawaye ne ke auren soyayya, ni auren kudi zan yi, Cewar amarya Habiba

Yadda ango ya fasa auren amarya bayan ta ki sanar da shi wanda ya siya mata IPhone 13 Pro Max

Wani matashi ya fasa auren budurwarsa bayan ta ki fada masa wanda ya siya mata waya kirar IPhone 13 Pro Max kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Dama an sa ranar aurensu ne kuma su na ta shirye-shirye, kwastam rannan tazo gida da waya IPhone 13 Pro Max.

Nan da nan masoyin nata ya bukaci sanin wanda ya siya mata wayar inda ta sanar da shi cewa dan uwanta ne.

Da ya ci gaba da bincike inda ya nemi sanin sunansa sai ta ki fadi wanda hakan yasa matashin ya fusata ya fasa auren.

An samu bayanin ne bayan abokin ango mai amfani da suna @Rita_Amy ya labarta yadda lamarin ya auku.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe