31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda Ɗan Chana ya yaudari Ummita cewa ya musulunta -Babbar ƙawarta

LabaraiYadda Ɗan Chana ya yaudari Ummita cewa ya musulunta -Babbar ƙawarta

Wata ƙawar Ummukulsum Sani Buhari (Ummita) matashiyar nan da Geng Quanrong ya halaka a Kano, ta bayyana cewa ya yaudari marigayiyar da cewa ya musulunta domin ta aure shi.

Daily Trust ta rahoto cewa Quanrong yanzu haka yana garƙame a hannun ƴan sanda bisa halaka Ummita a gidan iyayenta a ranar Juma’a. Ummita da Quanrong masoya ne.

Marogayiyar wacce bazawara ce, sun yi soyayya da Quanrong kafin tayi aure a farkon shekarar nan, sannan soyayyar su ta ɗora daga inda ta tsaya bayan sun rabu da mijinta.

Ta bayyana yadda ya yaudari Ummita

Da take magana da jaridar Daily Trust a a ranar Litinin, Rabia N. Garba, wacce ta bayyana kan ta a matsayin babbar ƙawar Ummita, tace sun san sunan Quanrong a matsayin Franke ne sannan ya gaya musu cewa ya mayar da sunan sa Faisal bayan ya musulunta saboda marigayiyar.

A ɗan sanin da nayi masa, mutum ne mai saurin fushi kan ƙananan abubuwa. Ko daɗewa akayi ba a mayar masa da saƙo ba yana fusata.

Eh zan iya cewa alaqar dake tsakanin su tayi kama da soyayya ko kawance, saboda marigayiyar ta san ba zata taɓa iya auren sa ba. Tayi iyakar bakin ƙoƙarin ta don ganin bai faɗa soyayyarta ba amma daga baya ta yanke shawarar su fara soyayya bayan yace ya musulunta.

Yayi iƙirarin cewa ya musulunta ne saboda ita wannan dalilin da yasa ta samu ƙarfin guiwar yin soyayya da shi. Har cewa ya fara koyon yadda ake yin Sallah.

Yadda ‘yata ta rasa ranta -Cewar mahaifiyar Ummita

A wani labarin na daban kuma mahaifiyar Ummita ta bayyana yadda ƴarta ta rasa ranta a hannun ɗan Chanan daya halaka ta.

Daily Trust ta ruwaito yadda aka kashe wata matashiya a unguwar Janbulo Quarters da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano a daren Juma’a.

Marigayiyar, wacce aka fi sani da ‘Ummita’ ta yi makarantar koyon aikin jinya da ungozoma a Kano. An yi jana’izar ta da misalin karfe 10 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe