LabaraiKu yi rijistar N600,000 don koyon addu'a ta musamman...

Ku yi rijistar N600,000 don koyon addu’a ta musamman kafin lokaci ya kure, Fasto

-

- Advertisment -spot_img

Wata fasto ‘yar kasar Amurka, Dr Juanita tana shan caccaka ta ko ina a kafafen sada zumuntar zamani yayin da ta bukaci $1499 ga mambobin cocinta don koya musu yadda ake addu’a, LIB ta ruwaito.

Kudin ya kai kimar N600,000 da doriya idan aka musanya su a kudin Najeriya. A cewarta, wannan kudi ne na koyon addu’a tsawon makwanni hudu wanda har katin shaidar iya addu’ar za ta bayar.

Nan da nan takardar tallar wannan addu’a ta take shirin koyarwa ta bazu a kafafen sada zumuntar zamani bayan ta wallafa a shafinta.

Kamar yadda ta rubuta:

Cibiyar koyar da addu’a za ta yi makwanni hudu ana koyar da addu’o’i. Za a yi ne sau bakwai kuma a ko wanne lokaci za a kwashe sa’o’i biyu ana yi. Kayi rijista yanzu!

Wurin koyarwar: Atlanta, GA. An takaita yawan jama’a!.”

Bayan gwaji da tantancewa, fasto ya rabawa ‘yan matan cocinsa takardun shaidar budurci

Wata cocin Afirka ta kudu ta kaddamar da gwajin budurci ga ‘yan matan da basu yi aure ba yayin da ta bayar da takardar shaida ga wadanda su ka yi nasara, LIB ta ruwaito.

An shirya tantancewar ne don bayar da kwarin guiwa ga mata don su kasance masu kamun kai a cikin al’umma.

Cocin mai suna Nazareth Baptist tana Ebuhleni, yankin arewacin Durban a Afirka ta kudu.

An tattaro bayanai akan yadda cocin ta shiya tantancewa ‘yan matan da basu yi aure ba na cocin wadanda su ka kai shekaru 18 zuwa sama don gane budurcinsu.

A taron na ko wacce shekara wanda cocin ta shirya, da zarar an kammala tantancewa za a bayar da takardar shaidar budurcin ga duk wacce aka tabbatar da budurcinta.

Sannan akwai wani farin zane da ake yi wa ‘yan matan a goshi idan aka tabbatar da kamun kan su.

Ana yin gwajin ne a tsakiyar ko wacce shekara kuma da zarar lokacin ya zagayo na wata shekara, takardar ta baci, sai har an sake gwajin a cikin cocin.

A wannan makon ne aka gabatar da gwajin na shekarar 2022/2023 sannan aka bayar da takardar shaidar ga matan da suka wuce gwajin.

A jikin takardar akwai sa hannun shugaban cocin Nazareth Baptist wanda shi ne ke gabatar da gwajin.

Hotunan da su ka bazu a yanar gizo sun nuna yadda ‘yan matan da su ka wuce gwajin lafiya su ke ta murmushi yayin da su ke rike da takardar shaidar.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you