A ranar Lahadi, 18 ga watan Satumban 2022 masu bauta na tsaka da ibada a cikin wata coci da ke kauyen Shikal cikin karamar hukumar Langtang ta kudu a Jihar Filato sai ga wani lamarin wanda ya janyo cikas a gare su kamar yadda Nigerian Pulse ta ruwaito.
Wata majiya daga kauyen ta sanar da The Nation cewa wasu masu shigar dodanni ne su ka afka coci ana tsaka da bauta su ka tada tarzoma.
Sun shiga ne da shirinsu inda su ka hau jibgar mutane kan mai uwa da wabi, tun daga kan masu bauta har faston ba su bari ba.
Nan da nan kowa ya fara neman hanyar tserewa don tsira daga cin na jakin. Hakan ya janyo asarar kujeru da sauran abubuwan da ke cikin cocin.
Bayan gwaji da tantancewa, fasto ya rabawa ‘yan matan cocinsa takardun shaidar budurci
Wata cocin Afirka ta kudu ta kaddamar da gwajin budurci ga ‘yan matan da basu yi aure ba yayin da ta bayar da takardar shaida ga wadanda su ka yi nasara, LIB ta ruwaito.
An shirya tantancewar ne don bayar da kwarin guiwa ga mata don su kasance masu kamun kai a cikin al’umma.
Cocin mai suna Nazareth Baptist tana Ebuhleni, yankin arewacin Durban a Afirka ta kudu.
An tattaro bayanai akan yadda cocin ta shiya tantancewa ‘yan matan da basu yi aure ba na cocin wadanda su ka kai shekaru 18 zuwa sama don gane budurcinsu.
A taron na ko wacce shekara wanda cocin ta shirya, da zarar an kammala tantancewa za a bayar da takardar shaidar budurcin ga duk wacce aka tabbatar da budurcinta.
Sannan akwai wani farin zane da ake yi wa ‘yan matan a goshi idan aka tabbatar da kamun kan su.
Ana yin gwajin ne a tsakiyar ko wacce shekara kuma da zarar lokacin ya zagayo na wata shekara, takardar ta baci, sai har an sake gwajin a cikin cocin.
A wannan makon ne aka gabatar da gwajin na shekarar 2022/2023 sannan aka bayar da takardar shaidar ga matan da suka wuce gwajin.
A jikin takardar akwai sa hannun shugaban cocin Nazareth Baptist wanda shi ne ke gabatar da gwajin.
Hotunan da su ka bazu a yanar gizo sun nuna yadda ‘yan matan da su ka wuce gwajin lafiya su ke ta murmushi yayin da su ke rike da takardar shaidar.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com