27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Jerin ƙasashe huɗu inda mace ke auren fiye da namiji ɗaya

LabaraiAl'adaJerin ƙasashe huɗu inda mace ke auren fiye da namiji ɗaya

baƙon abu bane jin cewa maza na auren mace fige da ɗaya, inda al’adu da addinai dama a duniya na goyon bayan wannan ɗabi’ar. Sai dai abin akwai ban mamaki jin cewa mace ta auri namiji fiye da ɗaya.

Ga jerin ƙasashen da mata ke auren namiji fiye da ɗaya wanda jaridar Tribune.ng ta tattaro.

Indiya

Ɗaya daga cikin ƙasashen da suka amince mace ta auri namiji fiye da ɗaya itace Indiya. Akwai ƙabilu da dama a ƙasar dake wannan ɗabi’ar. An dai fi samu a sassan Arewacin ƙasar a irin su Paharis na yankin Jaunsarbawar, yayin da a Kinnaur, Himachal mutane tsiraru sun yarda suna yi.

A matsayin su na tsatson Pachi Pandavas, sun yi amanna cewa yakamata su cigaba da wannan al’adar. Haka kuma a sassan Kudancin Indiya akwai ƙabilu irin su Toda a Nilgris, Najanad Vellala a Travancore, da wasu a ƙabilar Nair da suke yin wannan ɗabi’ar.

Kenya

A watan Agustan 2013 wasu maza a ƙasar Kenya suke yanke shawarar auren wata mace da dukkan su suke ƙauna. Dokokin ƙasar Kenya ba su haramta mace ta auri fiye da namiji ɗaya ba, hakan yasa ba za a iya hukunta mutanen dake yin hakan ba. Haka kuma ana samun irin wannan auren a tsakanin mutanen Massai na ƙasar Kenya.

China

Ba baƙon abu bane maza ƴan’uwan juna su auri mace ɗaya a tsakanin mutanen ƙabilar Tibet a yankin Arewacin ƙasar China da Indiya. Hakan yana a kan amanna da suka yi cewa yaro zai iya samun fiye da uba ɗaya, sannan idan kuma ƴan’uwan juna suka auri mace ɗaƴa, suna da dama daidai da daidai ta saduwa da ita.

Ana ƙarfafa wannan ɗabi’ar ne idan ahalin talakawa ne waɗanda ba su iya raba kadarorin su ga ƴaƴan da suke da iyaye maza daban. Hakan yasa suke auren mace ɗaya domin su riƙe ƙananan gonakin su da sauran kadarorin su.

Nepal

Nepal wata ƙasa ce yankin Kudancin nahiyar Asia wacce ke a yankin Himalayas. Tun a shekarar 1963 aka haramta mace ta auri namiji fiye da ɗaya, amma mutanen yankin Humla, Dolpa, da Kosi sun ɗauki al’adun su da muhimmanci fiye da doka. Akwai ƙauyukan da gabaɗaya irin waɗannan ahalin ne.

Irin wannan auren kuma ana samun sa a ƙabilun ƙasar na yankin Arewa, Arewa maso Gabas, irin su Bhote, Sherpa, Newbie, da sauran su.

Maasai: Kabilar da ake tofa wa amarya ‘Miyau’ a matsayin hanyar sanya wa aurenta albarka

Yayin da wasu kabilun duniya ke kallon tofa miyau a matsayin hanyar rashin kunya da cin mutuncin jama’a, kabilar Maasai da ke Kenya da arewacin Tanzania na kallon hakan a matsayin hanyar mutuntawa da sanya albarka.

Kabilar Maasai kaso 1 ce bisa 100 na mutanen Kenya da arewacin Tanzania, amma an san su da dabbaka al’adunsu tsawon lokaci wadanda su ka bambanta da na sauran jama’a.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe