27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Hukumar NDLEA ta kama kwalaben Akuskura 26,600 a jihar Kano

LabaraiHukumar NDLEA ta kama kwalaben Akuskura 26,600 a jihar Kano
Qasim Ademola NDLEA.jpeg

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama wani fitaccen mai hada abinda aka sani da Akuskura a Kano.

Jami’an sun kama Qasim Ademola, inda suka same shi da kwalaben a kuskura har guda 26,600 wanda aka tanada domin rarabawa a fadin jihohin Arewa.

An kama kayan ne a ranar Alhamis 15 ga watan Satumba a kan hanyar Zaria zuwa Kano,akan Gadar Tamburawa, a jihar Kano .Wanda yake hadawa mai kimanin shekaru 39 wanda yakasance dan asalin jihar Oyo ne an kama shi ne ,tare da wasu mutum uku a wani samame da aka yi.

Shugaban Hukumar ta NDLEA, Buba Marwa, ya yabawa jami’an rundunar ta Kano bisa yadda suke taka-tsantsan da jajircewa.

Ya kuma umarce su dama sauran ma’aikatan hukumar dake fadin kasar nan da su ci gaba da mai da hankali domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe