27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Dubban magoya bayan jam’iyyar PDP da NNPP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Sokoto

LabaraiDubban magoya bayan jam'iyyar PDP da NNPP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Sokoto
image 2 1140x570 1

Sama da Magoya bayan jam’iyyar PDP da NNPP 9,800 a karamar hukumar Goronyo ne suka fice daga jam’iyyarsu zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Bashar Abubakar, mataimaki na musamman na kankafafen yada labarai ga shugaban jam’iyyar APC na jihar, Aliyu Wamakko ya fitar ranar Lahadi a Sokoto.

Mista Abubakar ya ce wadanda suka sauya sheka sun hada da dan takarar majalisar dokokin jihar NNPP , Maniru Malami, tare da daruruwan magoya bayansa.

Abubakar ya ce Malami ya fice daga jam’iyyar ne tare da daukacin magoya bayansa na hukumomi da mambobin kwamitin zartarwa na gundumomi 11.

Haka kuma Sabbin wadanda suka tsallaka jam’iyyar APC sun hada da tsohon dan takarar majalisar jiha, Shehu Dan-Tsamaye, da kuma sakataren kudi na yanzu, Hamza ‘Yar-Dole.

Sauran sun hada da shugaban kungiyar masu unguwanni na yankin, Amadu Dan-Kansila, da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP, irin su Hamisu Mai-Alewa.

Mista Abubakar ya ce dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu shi ne ya tarbe su.

Inda dan takarar gwamnan ya bayyana cewa sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC alama ce dake nuna jam’iyyar ta sami karbuwa.

Mista Aliyu ya ce, “PDP a jihar Sokoto ta gaza cika dukkan alkawarukan da ta yi wa al’ummar jihar tun shekarar 2019.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe