37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Ƴan bindiga da dama sun halaka bayan sojin sama sun yi luguden wuta sansanin Bello Turji

LabaraiƳan bindiga da dama sun halaka bayan sojin sama sun yi luguden wuta sansanin Bello Turji

Rundunar sojin saman Najeriya tayi luguden wuta a sansanin riƙaƙƙen ɗan ta’adda Bello Turji, a ranar Asabar a jihar Zamfara, inda ta hari wasu daga cikin na hannun daman sa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a samu cikakkun bayanai ba dangane da harin amma jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan bindiga da dama sun halaka a harin.

Ana kyautata zaton cewa harin ya ritsa da Bello Turji

Sai dai Bello Turji wanda a lokacin yake a ɗaya daga cikin maɓoyarsa a dajin Fakai cikin ƙaramar hukumar Shinkafi, ya tsere.

Majiyoyi sun tabbatarwa da jaridar cewa ƴan bindiga da dama sun samu raunika a yayin harin sannan wasu da dama sun halaka.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun bayyana cewa Bello Turji na daga cikin waɗanda harin ya ritsa da su amma wata majiya tace ya sha da ƙyar tare da wasu daga cikin yaran sa.

Sojoji sun ƙara ƙaimi wuri kai hare-hare a cikin ƴan kwanakin nan, inda suke fatattakar ƴan bindiga da suke addabar mutane a ƙasar nan.

Bello Turji, wanda yake da iko kan ƴan bindiga da dama, ya na kan gaba wurin kai hare-hare a jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa masa Yamma.

Hare-haren na Bello Turji sun janyo asarar rayuka da dama da dukiyoyin jama’a, yayin da wasu aka tilasta musu rabuwa da matsugunan su inda suka koma ƴan gudun hijira.

Ƴan sanda sun cafke masu safarar makamai da kayan sojoji ga ƴan bindiga a Zamfara

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wasu ɓata gari masu ba ymƴan bindiga bayanai da safarar makamai da kayan sojoji a jihar Zamfara.

Hukumar ƴan sandan jihar Zamfara ta cafke masu bada bayanai da safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar.

Kakakin hukumar, Mohammed Shehu, shine ya sanar da hakan yayin zantawa da ƴan jarida a ranar Asabar.

A cewar sa, an cafke mambobin wata tawagar mutum shida ta masu bada bayanai wacce ta haɗa Abubakar Mainasara, Babangida Soja, Jamilu Lawali, Lawal Ibrahim, Surajo Idris da Amadu Rufa’i a ranar Juma’a.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe