27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ƴan sanda sun cafke masu safarar makamai da kayan sojoji ga ƴan bindiga a Zamfara

LabaraiƳan sanda sun cafke masu safarar makamai da kayan sojoji ga ƴan bindiga a Zamfara

Hukumar ƴan sandan jihar Zamfara ta cafke masu bada bayanai da safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar.

Kakakin hukumar, Mohammed Shehu, shine ya sanar da hakan yayin zantawa da ƴan jarida a ranar Asabar.

A cewar sa, an cafke mambobin wata tawagar mutum shida ta masu bada bayanai wacce ta haɗa Abubakar Mainasara, Babangida Soja, Jamilu Lawali, Lawal Ibrahim, Surajo Idris da Amadu Rufa’i a ranar Juma’ah. Jaridar The Cable ta rahoto.

A ranar 12 ga watan Satumba 2022, an cafke mutanen da aka lissafo waɗanda mambobi ne a wata hatsabibiyar ƙungiyar masu bada bayanai ga ƴan bindiga waɗanda suke haɗa baki suna addabar mutanen ƙananan hukumomin Gusau, Kaura Namoda, Tsafe, da Bungudu.

Ayyukan da waɗannan ɓata garin ke yi shine bada bayanai ga ƴan bindiga ta yadda za su samu sauƙin kai hare-hare da satar mutane domin kuɗin fansa.

Haka kuma suna amsar miliyoyin nairori a hannun ƴan bindiga domin samar musu da kayan sojoji da makamai.

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin Abubakar Mainasara ya gayawa ƴan sanda cewa ya karɓi N850,000 a hannun ƴan bindiga domin samar musu da kayan sojoji.

Ya bayar da kuɗin ga Babangida wanda aka fi sani da Major, wanda ya haɗa baki da wani tela mai suna Jamilu Lawali domin samar da kayan sojojin wanda daga ƙarshe aka kai wa ƴan bindigan.

A cewar kakakin ƴan sandan jihar Zamfara

Ƴan bindiga sun sake kai wani sabon hari, sun halaka wani ɗan kasuwa da sace mutane da dama a Katsina

A wani labarin na daban kuma ƴan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Katsina.

Ƴan ta’adda sun sake kai wani sabon hari a ƙauyen Bakiyawa na ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina.

Harin ya auku ne a ranar Laraba inda ƴan bindigan suka halaka wani ɗan kasuwa mai sayar da hatsi mai suna Tukur Makeri, sannan kuma suka sace wasu mutanen da dama a ƙauyen.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe