27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Wani minista a Indiya yayi kiran da a rushe masallatai a ƙasar

LabaraiWani minista a Indiya yayi kiran da a rushe masallatai a ƙasar

Wani minista a ƙasar Indiya yayi kiran da rushe masallatan dake a kusa da majami’o’i a ƙasar.

Sanjay Nishad wanda shine shugaban jam’iyyar Nishad a jihar Uttar Pradesh yace “Dole ne a cire masallatan dake kusa da majami’o’i”

Haka kuma ministan ya ƙara da cewa:

Makarantu na koyar da tsatstsauran ra’ayin addini. Akwai alaƙa a tsakanin waɗannan makarantun da ta’addanci.

Ministan ya dai yi wannan furucin ne a wurin rangadin duba makarantun addinin musulunci da ake a ƙasar. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

A ranar Laraba ministan ya ziyarci Baghpat inda yace:

Ana duba makarantun ne domin a zamanantar da su ta yadda yara za su koyi darussan zamani su zama likitoci, injiniyoyi da jami’an IAS. Saboda haka malamai yakamata su goyi bayan dubiyar da ake.

Shugabanni za su ilmantar da ƴaƴan su a wurare keɓaɓɓu, yayin da talakawan musulmi za su samu ilmin addini kawai.

A cewar Nishad, malaman addinin musulunci sun mayar da musulmai talakawa, sannan jam’iyyun adawa na yaɗa farfagandar addini a ƙasar.

Ana yawan tsangwamar musulmai a Indiya

Musulmai a ƙasar Indiya dai na yawan fuskantar tsangwama da barazana daga wurin jamivan gwamnati a ƙasar wacce ke ƙarƙashin jagorancin masu tsananin kishin addinin Hindu. Firaminstan ƙasar Narendra Modi bai yi wani kataɓus ba na ganin cewa sun dai na fuskantar hakan, hasalima sai dai ƙara tunzara ƙaruwar hakan da yake yi.

Kotu ta bada belin ɗan majalisar da yayi ɓatanci ga Annabi (SAW) a Indiya

A wani labarin na daban kuma, wata kotu a ƙasar Indiya ta bayar da belin ɗan majalisar da yayi ɓatanci ga Annabi (SAW). Kotun ta dai bayar sa belin sa ne bayan an gurfanar da shi a gabanta.

Wata kotu a birnin Hyderabad na ƙasar Indiya a ranar Talata, ta bayar da belin ɗan majalisar jam’iyyar Bharatiya Jhanati Party, BJP, T. Raja Singh, bayan da aka gurfanar da shi a gaban ta.

An dai gurfanar da ɗan majalisar ne bayan an cafke shi a ranar Talata bisa laifin yin wasu kalamai na ɓatanci akan fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe