
Ofishin jakadancin Burtaniya da ke Harare a ranar Alhamis ta ce wasikar da aka ce fadar Buckingham ta aikawa shugaban kasa Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe na hanashi halartar jana’izar Sarauniya karya ce.
Ofishin jakadancin ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter yana mai cewa, “An gayyaci shugaba Mnangagwa don halartar jana’izar mai martaba Sarauniya Elizabeth ta biyu a Westminster Abbey ranar Litinin.”
“Wasiƙar da ke yawo kan batun hanashi izinin halarta karya ce,” in ji shi, tare da haɗa kwafin wasiƙar da aka yada a shafukan sada zumunta.
Jakadiyar Burtaniya a Zimbabwe, Melanie Robinson, a ranar Juma’a, ta saka hoton Mista Mnangagwa a lokacin da yake sanya hannu kan littafin ta’aziyya a ofishin jakadancin.
Mista Mnangagwa ya wallafa, hotonsa a shafinsa na twitter yana sanya hannu tare da jakadan.
“Abin alfahari ne na sanya hannu kan littafin ta’aziyya ga marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu a Ofishin Jakadancin UK dake Zimbabwe da kuma ba da goyon baya ga @HMAMelanier,wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A cewar wasikar karya da aka ce an rubuta a madadin Sarki Charles III wasikar ta bayyana cewa bata gayyace Mista Mnangagwa zuwa halartar jana’izar sarauniyar a Westminster Abbey ba saboda takunkumin tafiye-tafiye da kasashen Yamma suka sanya masa da sauran jami’an gwamnati da kuma dalilan take hakkin dan Adam.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com