Tuni har ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya fara rubuta sunayen mutane ciki har da na ƴan adawa waɗanda zai yi aiki da su idan ya lashe zaɓe.
Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku, Charles Aniagwu, shine ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise kan rikicin cikin gida na PDP. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ko a ina kake, idan har kana da rawar da zaka iya takawa, Atiku zai nemo ka ba tare da la’akari da wani yanki ka fito ko kuma addinin da kake yi.
Shugaban ƙasa baya buƙatar ya zama likita kafin ya iya magance matsalolin fannin lafiya, baya buƙatar ya zama injiniya kafin ya samar tsare-tsare na ɓangaren gine-gine.
Abinda shugaban ƙasa yake yi shine ya tattara irin waɗannan mutanen da suke da wannan ilmin. A yanzu da nake magana da kai, ina sane da abubuwa sosai. Tuni har Atiku ya fara rubuta sunayen ƴan Najeriya wasu daga ƙasashen waje sannan da waɗanda ba ƴan jam’iyya bane da yake son yayi aiki tare da su.
Abin a bayyane yake cewa lallai idan har ana son ceto Najeriya, ba ƴan jam’iyyar ka bane kaɗai za su bada gudunmawa.
Ya kawar da tsoron da wasu keyi na Atiku zai siyarwa da abokan sa kamfanonin gwamnati
Da yake magana akan shirin Atiku na siyar da kadarorin gwamnati waɗanda ba su yin wani abin a zo a gani, Aniagwu ya kayar da tsoron da wasu ke yi na cewa kamfanonin gwamnati za su ƙare a hannun abokan Atiku idan yaci zaɓe.
Yace kusan dukkanin ƴan kasuwan Najeriya abokan Atiku ne, saboda shima ɗan kasuwa ne.
Sai dai Aniagwu ya bada tabbacin cewa za a siyar da kamfanonin gwamnati da basu wani abin arziƙi ga mutanen da suka cancanta domin samun nasarar siyar da su.
Ƙuri’un Arewacin Najeriya na Kwankwaso ne, Atiku ba tsaran sa bane -Abdulmumin Jibrin
A wani labarin na daban kuma, Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa Atiku ba zai iya kafada da kafada da Kwankwaso ba wurin samun ƙuri’un ƴan Arewa.
Kakakin jam’iyya mai kayan marmari NNPP, Abdulmumin Jibrin, yace ko kaɗan Atiku Abubakar ba zai iya kama kafar Kwankwaso ba, domin ba tsaran sa bane.
Jaridar Daily Trust ta ambato Jibrin na bayyana hakan ne yayi wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin su na Siyasa a yau.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com