Wata ‘yar kasuwa, Monica Gambo, a ranar Juma’a ta maka mijinta, Yakubu Gambo gaban kotun Nyanya da ke Abuja akan kin bata hakkinta na aure, Nigerian Pulse ta ruwaito.
Ya bayyana yadda ya tare a wurin karuwai yana yin masha’arsa yadda yaga dama. Ta kara da cewa:
“Yana hana ni hakkin aurena don haka ba zan iya ci gaba da zama da shi ba.”
Ta ci gaba da shaidawa kotu yadda mijinta yayi yunkurin halaka ta don kwashe dukiyarta.
Ta bukaci kotu ta raba aurensu ta kuma umarci mijinta da ya kwashe komatsansa ya bar mata gidanta.
Mijin nata, Yakubu Gambo, wanda tela ne ya musanta duk zargin da take yi masa. Daga nan ne Alkalin kotun, Shettima Mohammed ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Satumba.
A rabamu, mijina ba ya sassauta min a shimfidar aure, ba dare ba rana, matar aure ga kotu
Wani magidanci, Rasheed Afeez ya maka matarsa a gaban kotun Ibadan inda yake bukatar a raba aurensu saboda matarsa ba ta barinsa ya kwanta da ita, Daily Trust ta ruwaito.
Afeez, wanda ma’aikacin banki ne kuma malamin makarantar firamare, ya bayyana cewa tun kafin aurensu su ka yi gwajin jini amma kwatsam sai ta dena barinsa ya hada shimfida daya da ita.
A kara da cewa:
“Yanzu haka Nafisat yawon bin otal iri-iri take yi.” Yayin mayar da martani, Nafisat wacce ma’aikaciyar asibiti ce, sannan tana da yara biyu, ta amince a raba aurensu mai shekaru tara saboda Afeez yana damunta da jaraba.”
Ta ci gaba da cewa:
“Mai girma mai shari’a ya mayar da ni kamar ‘yar tsana, kusan kullum neman mu kwanta ba tare da ya duba illar hakan ga lafiyarmu yake yi.
“Bai damu da halin da nake ciki ba, kawai son kai ne da shi. Idan naki amincewa sai ya tursasa ni kwanciya da shi.
“Akwai daren da Afeez ya bukaci mu kwanta duk da mun yi fada. Ni kuma naki amincewa daga nan ne yaso ya tursasa ni, na yi sauri na tsere kicin inda ta dauki wuka don in kare kaina.
“Sannan ina tsoron ci gaba da haihuwa da shi saboda kada in haifi mai lalurar sikila. Don daya daga cikin yaranmu yana fama da cutar. Daga ni har Afeez duk AS ne. Bai damu da siya wa danmu da ke fama da lalurar magani ba.”
Ta ci gaba da bayyana rashin sanin mutuncin kansa da yake yi, don a cewarta ba ya daukar dawainiyar matarsa da ta yaransa.
Alkalin kotun, Mrs S. M Akintayo ta dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Satumba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com