
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki domin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ke yi.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Shugaban tare da zababbun mambobin Pro-Chancellor na Jami’o’in Tarayya a ranar Juma’a a garin Abuja.
Ya ce ba tare da sake maimaita abinda aka riga aka sani ba, “Zan sake dubi ga lamarin kuma zan dawo gare ku.”
Farfesa Nimi Briggs ne ya jagoranci shugaban jami’o’i zuwa taron.
Mista Briggs ya ce sun zo ne domin ganawa da shugaba Buhari a matsayinsa na “Shugaban kasa kuma Babban Kwamanda, uban kasa, sannan kuma Maziyarcin Jami’o’in Tarayya.”
Ya kara da cewa, duk da matsalolin da aka samu na shafe watanni bakwai ana yajin aiki makomar tsarin jami’a a kasar yana da kyau”.
Inda ya yi misali da jami’ar Ibadan wacce ta kasance cikin jerin jami’o’i 1,000 na farko a duniya.
Shugabannin jami’o’i sun kuma nemi a sake duba hukuncin Gwamnati na Ba Aiki, Ba Biya.
Sun yi alkawarin cewa malamai za su rama lokacin da aka bata da zarar komai ya daidaita an bude makarantu.
Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Opiah, ya ce duk wani abinda ya kamata ace Gwamnati Tarayya ta yi na ganin cewa “an kawo karshen yajin aiki,tayi amma kungiyar ta yi biris.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adires
N