31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Nayi nadamar rashin yin saurayi a rayuwata -Tsohuwa ƴar shekara 92 ta koka

LabaraiNayi nadamar rashin yin saurayi a rayuwata -Tsohuwa ƴar shekara 92 ta koka

Wata tsohuwa mai shekara 92 a duniya, Xaveline, daga ƙasar na rayuwar kadaici sannan babban dana sanin ta a rayuwa shine rashin samun saurayin da zai aure ta.

Tsohuwar matar dai na da ƴan’uwa 14 waɗanda duk sunyi aure sun ƙyale ta a gida.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa tsohuwar ta shaidawa tashar Afrimax a Youtube cewa:

Na rayu tare da iyaye na, sun sha gayamin cewa suna jiran ranar da zanyi aure na samar musu da jikoki.

Nima na so hakan, amma abin takaicin sun rasu banyi aure ba kuma kamar nayi tsufa da na samu saurayi.

Na zama saura ni kaɗai kawai hakan ya sanya na yanke shawarar komawa wurin ƴar autar mu.

Wasu daga cikin ƴan’uwa, abokai da makwabta na ganin cewa kamar maita na da hannu a rashin auren da tsohuwar tayi.

Ta koma rayuwa tare da ƴar’uwarta

Bayan rasuwar iyayenta, Xavaline ta koma rayuwa da ƴar autar ɗakin su mai suna Fatuma Justlene, wacce ta shiga damuwa cewa rashin lafiya zai iya kamata kuma ba wanda zai kula da ita.

Mun kasa gano dalilin da yasa hakan, ƙila kawai bata da sa’a ne haka rayuwar ta zo mata. A cewar Justlene

An nemawa tsohuwar magani amma ba a dace ba

An yi watsi da batun maita domin an kai ta wurin bokaye amma hakan bai yi aiki ba domin bata samu mijin aure ba.

An kuma kai tsohuwar coci amma duk da hakan ba a samu dacewa ba. Kwatsam kuma cikin ƴan shekarun baya-bayan nan kawai sai kafafuwan ta suka fara kumburi wanda hakan ya sanya take fama da azababben ciwo.

Yadda matashi mai shekaru 25 ya cika bujensa da iska kwanaki kadan bayan auren tsohuwa mai shekaru 65

A wani labari na daban kuma wani matashi ya cika wandonsa da iska kwanaki kaɗan bayan ta auri wata tsohuwa ƴar shekara 65.

Wata dattijuwa mai shekaru 65 ta bayyana gaban kotu inda take cigiyar angonta wanda matashi ne mai shekaru 25 yayin da take da shekaru 65, Dala Fm ta ruwaito.

Kamar yadda ta sanar da kotu, ko kazar amarci da sauran kayan makulashe bai bata ba, bata san dalilinsa na yin hakan ba, bayan auratayya ta shiga tsakaninsu ya gudu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe