31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Duk namijin da ya kula hankalin matarsa ya karkata kan yara, ya kara aure, Jarumi Ibrahim

LabaraiDuk namijin da ya kula hankalin matarsa ya karkata kan yara, ya kara aure, Jarumi Ibrahim

Wani jarumin finafinan kudu, Ibrahim Chatta ya bai wa maza masu aure shawara dangane da yadda za su bullo wa matansu da zarar sun kula hankulansu ya koma kan yaransu.

A cewarsa, duk namijin da ya kula matarsa ta fi son yaransa akan shi, yayi gaggawar yin aure don ya samu kulawa ta musamman a wurin amarya.

A cewarsa, matsawar namiji yana so ya ci duniyarsa da tsinke, to ya kara aure don hakan zai sanya hankulan duk matan ya koma tunanin yadda za su yi su kyautata masa.

Ya bayyana wannan ra’ayin a bidiyon da shafin Instablog9ja na Instagram ya nuna:

Ga bidiyon a kasa:

Ya kamata a dinga rufe namijin da bai iya gamsar da matarsa shi daya a daki yayi wata 3, Obi

Wani jarumin finafinai, Ernest Obi ya bayar da wata shawara a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumban 2022 yayin da ya ke tsokaci dangane da matar da ta da aka yi garkuwa da mijinta saboda ba ya gamsar da ita a gadoNigerian Pulse ta ruwaito.

In har dagaske ne hujjar da ta bayar, ina bin bayanta. Ya kamata a garkame duk namijin da ya gaza gamsar da diyar mutane a daki yayi watanni uku,” kamar yadda ya wallafa.

Shiyasa matata ke kiransa…Aikin miji… gaskiya ban san inda ta sami sunan nan ba…Amma na yarda da wannan sunan,” daga nan ya kwashe da dariya.

Sai dai a cewar jarumin, bai amince da batun garkuwa da wani ba ta ko wacce hanya. Amma maganar gaskiya ba daidai bane namiji ya kasa gamsar da matarsa.

Idan ba a manta ba, matar mai suna Joy ta ce akwai dalilin da ya sanya tayi garkuwa da mijinta, Ebong, dan asalin yankin Ntak Obio Akoa na karamar hukumar Oruk Anam.

Ta bayyana yadda bayan rashin gamsar da ita a shimfida da mijinta yake yi, ba ya kawo musu abinci.

Ta ci gaba da cewa:

Ina yin ‘yan kananun ayyuka don in tallafawa yaranmu. Don haka ne na kitsa yin garkuwa da mijina don in samu kudin yin hidindimu.”

Sai dai ban sami kudin fansar ba duk da na yi garkuwa da shi,” a cewarta.

Joy ta ambaci wani Udo Moji, wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar da tasa su yi garkuwa da mijinta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe