Wasu musulmai sun shirya addua da sadaka ta kwana takwas ga sarauniya Elizabeth, wacce ta mutu cikin ƴan kwanakin nan.
Wani shahararren mai wasan barkwanci da ban dariya a Najeriya, Abdulgafar Ahmad Oluwatoyin, wanda aka fi sani da Cute Abiola, shine ya shirya adduar ga sarauniya Elizabeth. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Adduar da Cute Abiola ya shiryawa sarauniya Elizabeth dai ta ɗauki hankulan mutane sosai a yanar gizo inda suka tofa albarkacin bakin su.
Cute Abiola ya sanya wani bidiyo inda aka gan shi tare da wasu mata suna addua ta kwana takwas ga sarauniyar Ingila, sarauniya Elizabeth II.
A cikin bidiyon da ya sanya a shafin sa na Instagram, akwai wasu mata sanye da tufafi iri ɗaya wanda hakan ba baƙon abu bane a wurin musulmai Yarabawa, sun taru suna adduar kwana takwas (Fidau) ga sarauniyar ta Ingila wacce ta rigamu gidan gaskiya.
Bidiyon adduar da aka yiwa sarauniya Elizabeth ya jawocece-kuce
Mutane da yawa sun yi tsokaci akan bidiyon inda suke tambayar ko akwai wata dangantaka ne tsakanin Abiola da sarauniyar wacce ta sanya ya shirya mata adduar kwana takwas.
@sunkanmi_omobolanle ya rubuta:
Inye kaga fa ƙanin Charlie
@the_real_simigold ya rubuta:
Kana da matsala… Ka tabbata kuwa baka shaye-shaye.
@ykmoore_ ya rubuta:
Meye naka a ciki
@blazeisfunny ya rubuta:
Elisa na can na farin ciki yanzu haka.
Jami’an tsaron Saudiyya sun yi ram da mutumin da ya sadaukar da Umararsa ga Sarauniyar Ingila, Elizabeth
A wani labarin na daban kuma, jami’an tsaro a Saudiyya sun cafke wani mutum da ya sadaukar da Umarar sa ga sarauniya Elizabeth II. Mutumin dai ya garzaya ƙasar Saudiyya musamman domin yayi Umara saboda sarauniya Elizabeth II.
Kamar yadda jami’an tsaron Saudiyya su ka bayyana, sun kama wani mutum wanda yaje Makka musamman don yayi umara saboda Sarauniya Elizabeth II, The Islamic Information ta ruwaito.
Kamar yadda rahotanni su ka nuna, mutumin dan Yemen ne kuma ya saki bidiyonsa a ranar Litinin a babban masallacin Makka na Ka’aba wanda aka haramta wa wadanda ba musulmai ba zuwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com