34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ya ki hakuri in kile, inji budurwar da saurayinta ya rabu da ita lokacin tana sanya Hijabi

LabaraiYa ki hakuri in kile, inji budurwar da saurayinta ya rabu da ita lokacin tana sanya Hijabi

Wata budurwa wacce musulma ce ta bayyana wa duniya yadda saurayinta ya rabu da ita lokacin tana sanya hijabi inda tace ya kasa hakuri ya kile, Legit.ng ta ruwaito.

A cewarta, saurayinta ya so ta dena sanya hijabi amma ta ki a lokacin, ashe da ya kara mata lokaci da ta waye ta zama daidai da yadda yake so.

Hotunan da Hassanat Abass Abiodun ta wallafa na lokacin tana sanya hijabi sun yi matukar bai wa mutane da dama mamaki.

A cewarta, lokacin saurayinta ya rabu da ita ne saboda rikon addinin ta ya yi yawa. Nan da nan aka fara yada hotunan wanda ta shiga gasar ci gaba da jama’a su ke ta yi.

Sai dai a bangarenta ta sha caccaka kwarai inda mutane musamman musulmai su ka dinga kallon lamarin a matsayin ci baya.

Bayan ta wallafa a shafinta na TikTok, a tsofaffin hotunanta an ga yadda ta rufe jikinta rijif da hijabai wadanda su ka wuce gwiwarta.

Daga bisani kuma ta wallafa sauran hotunanta na yanzu sanye da matsatstsun kaya masu bayyana surarta.

Tsokacin jama’a a karkashin bidiyon

Nan da nan mutane da dama su ka dinga tsokaci karkashin bidiyon.

houseofdoughnuts tace:

Allah ya yafe miki amma ni dai ban ga abin alfahari ba anan.”

daudajnr145 yace:

Muna fatan Ubangiji madaukakin sarki ya shiryar da ke hanya madaidaiciya.

user3906244500619 tace:

“Daga halayya ta kwarai zuwa mummuna. Ya kamata ma ki ji kunya.”

janine tace:

Yar uwa babban burin kowa shi ne shiga Aljannah. Allah ya mayar da ke hanya madaidaiciya.”

Abdul Rasaq yace:

Dama baki yi amfani da wadannan hotunan ba. Ba komai ake nunawa ba. Ubangiji ya shiryar damu.

ssssaiwaaa tace:

Kash…kin fi kyau a lokacin kina riko da addini. Bai da ce ki sauya saboda wani ba. Allah ya shirye mu.”

Masha Allah: Fatima Payman, musulma mai Hijabi ta farko da aka zaba a matsayin Sanata a kasar Australia

Mace ta farko da ke sanya Hijabi ta ja hankalin jama’a bayan ganin ta lashe zabe a matsayin ‘yar majalisar dattawa a yammacin Australia ranar 20 ga watan Yuni, wanda hakan yasa ta kafa tarihin zama sanata ta farko mai sanya Hijabi a gabadaya tarihin kasar Australia kuma sanata mai mafi karancin shekaru, Theislamicinformation.com ta ruwaito.

Sunanta Fatima Payman, shekarunta 27 kuma asali ‘yar gudun hijira ce wacce ta baro Afghanistan zuwa Australia lokacin tana da shekaru 8 da haihuwa.

A jawabinta na farko a mukamin, cike da hawaye Payman ta bayyana farincikinta akan yadda mahaifinta yayi sadaukarwa mai yawa akanta, wanda ya zauna a Australia a matsayin dan gudun hijirar Afghanistan kuma ya rasu a 2018.

Cike da alfahari Payman tace wa yayi zaton matashiya mai karancin shekaru da aka haifa a Afghanistan kuma diyar dan gudun hijira zata taba zama ‘yar majalisa a Australia.

Payman ta ci gaba da bayyana yadda mahaifinta ya sadaukar da kansa wurin gina rayuwarta. Ta bayyana yadda yayi kananun ayyuka kamar direban tasi, mai gadi da sauransu duk don tara kudin da zai kula da ita da kanninta uku.

Sai dai a cewarta duk da dagewar mahaifinta don ganin sun samu rayuwa mai inganci shi bai dage akan kansa ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe