27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Asibitin koyarwa na jami’ar Benin sun rike gawar wata yarinya akan kudin jinya Naira 400,000

LabaraiAsibitin koyarwa na jami'ar Benin sun rike gawar wata yarinya akan kudin jinya Naira 400,000
University of Benin Teaching Hospital Benin Edo State 1140x570 1

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) sun rike gawar wata yarinya ‘yar shekara 12 mai suna Glory Ekeleyede, saboda iyayenta sun gaza biyan kudin asibiti.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa yarinyar ta,rasu ne a asibitin a ranar 15 ga watan Yuli.

NAN ta samu labarin cewa kudin jinyar ya kai kimanin N400,000.

Wata majiya ta shaida cewa rashin biyan kudin jinyar shi ne ya tilasta wa asibitin kwace gawar .

Mahaifin marigayiyar Samson Ekeleyede, mai shekaru 66, ya koka da yadda ciwon ’yarsa ya jefa su cikin matsalar kudi.

Ya ce bashin kudi suke ci don biyan kuɗaɗen asibiti da sauran hidima.

Mista Ekeleyede wanda ya kasance Manomine, matarsa kuma ‘yar kasuwa ce, ya ce da kyar suke samu suci abinci saboda yadda suke kashe kudi akan jinyar ‘yar su.

“Ina sana’ar dinki, da kuma wasu kananan ayyuka da nake don ciyar da iyalina.Matata tana sayar da tumatur da barkono a kasuwa da haka muke lallaba rayuwa” inji shi.

Dangane da kokarin da ya yi tun rasuwar ‘yar sa, Mista Ekeleyede ya ce “yar ta rasu tun ranar 15 ga watan Yuli, kuma tun a lokacin tana dakin ajiyar gawa.

“Na yi ta rokon su; saidai sun bayyana min cewa suma ba hurumin su ba ne. Saboda haka dole sai na biya. Sun ce amfani da iskar oxygen da suka yi shi ne ya sa kudin ya yi yawa.

“Da ace tana da rai nema da da sauki. Sun dage dole sai na biya na yi ta binsu su bani gawar don aje s binne sunki.

“Na gaya wa wani baban mu na coci. Abin ya ba shi mamaki, ya rubuta wa gwamnati takarda. Ya ce in kai ofishin mataimakin gwamna.

“A lokacin dana kai takardar gwamnan yana hutu; mataimakin sa ne ke bakin aiki. Ranar da na kai a ranan ne Gwamna Obaseki ya dawo daga hutun sa. Na ba PRO.

“Dama shi aka ce in bawa. Tun daga lokacin, muna jira, har yanz shiru”.

Da aka tuntubi mai magana da yawun UBTH, Uwaila Joshua, ta ce “duk wanda aka yiwa jinya dole zai biya kudi”.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adires

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe