32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Ƙuri’un Arewacin Najeriya na Kwankwaso ne, Atiku ba tsaran sa bane -Abdulmumin Jibrin

LabaraiƘuri'un Arewacin Najeriya na Kwankwaso ne, Atiku ba tsaran sa bane -Abdulmumin Jibrin

Kakakin jam’iyya mai kayan marmari NNPP, Abdulmumin Jibrin, yace ko kaɗan Atiku Abubakar ba zai iya kama kafar Kwankwaso ba, domin ba tsaran sa bane.

Jaridar Daily Trust ta ambato Jibrin na bayyana hakan ne yayi wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin su na Siyasa a yau.

Kwankwaso zai lashe ƙuri’un Arewacin Najeriya

Tsohon ɗan majalisar tarayyar yace Kwankwaso zai lashe ƙuri’un Arewa sannan kuma zai samu ƙuri’u masu yawa daga yankin Kudancin ƙasar nan.

Jibrin yace:

Ɗan’uwa na Daniel Bwala, yayi maganar PDP tana a ko ina, amma ta yaya? A 2015 sun sha kaye, a 2019 sun ƙara shan kaye. A 2023 ma kayen za su ƙara sha. Ɗan takarar su (Atiku) ba tsaran Kwankwaso bane a Arewacin ƙasar nan.

Ya bayyana matsalar da APC ke fuskanta

Idan ana magana kan APC, abinda APC bata son a sani shine sun cinye zaɓukan baya ne saboda suna samun ƙuri’u miliyan 12 saboda Buhari. A yau waɗannan ƙuri’un miliyan 12 babu su.

A karon farko cikin shekara takwas ko goma, za su fara zaɓen shugaban ƙasa ba su da komai. A ina za su samo ƙuri’u miliyan takwas? Wannan shine abinda shugabannin APC ba su magana akai. Daga farko za su fara.

Nuna min mutum ɗaya a APC wanda zai iya samar musu da yawan waɗannan ƙuri’un. Ba za su iya samu ba. Maganar gaskiya itace ƙuri’un Arewa na Kwankwaso ne sannan zai samu ƙuri’u masu yawa a yankin Kudancin ƙasar nan.

Shugabancin Kwankwaso zai kawo waraka a Najeriya -Idahosa

A wani labarin na daban Kuma, an bayyana shugabancin Rabiu Musa Kwankwaso. Matsayin abinda zai kawo waraka a Najeriya.

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP), Bishop Isaac Idahosa, ya bayyana tikitin ubangidan sa, Dr Rabiu Kwankwaso, a matsayin “tafiyar waraka” wacce zata ciro ƙasar nan daga halin ha’ula’in da take ciki.

A cewar sa, za a samu zaman lafiya, cigaba da kwanciyar hankali ne kawai idan akwai gaskiya da adalci, waɗanda yace takarar Kwankwaso zata nuna hakan

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe