Jarumin finafinan Kannywood, Tahir Muhammad Fagge ya bayyana sanadiyyar da ya sanya ya fara rawa a gidan gala kamar yadda aka dinga yada bidiyonsa a kwanakin nan.
A wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da shi, ya bayyana yadda Ubangiji ya jarabce shi da mummunan ciwon zuciya wanda ba ya da kudin da zai nemi lafiyarsa.
A cewarsa, ba ya rasa wadanda kai tsaye zai tambaya kudi bane, akwai mutane irin su Ali Nuhu, amma yana matukar jin nauyin yin hakan.
Ya ce ya yi wata tafiya ne inda ya bar iyalinsa a mawuyacin hali, bayan ya dawo su ka hadu da Ali Nuhu wanda ya siya masa sabuwar dalleliyar waya.
Bayan ya koma gida kuma ciwo ya kwantar da shi. Ganin hidimar da yayi masa ne yaji nauyin tambayarsa. Wanda hakan yasa ya fara fafutukar neman yadda zai yi ya samu lafiya.
Bayan asibiti inda aka duba lafiyarsa sai ya je neman taimako wurin mawaki Rarara, wanda ya bashi N20,000, Abubakar Bashir Maishadda ya bashi N20,000 sai Abdul Amat ya bashi N15,000, a lokacin yana bukatar dubu dari biyu da doriya.
Yana cikin yanayin ne aka gayyashi taron bude wani gidan rawa wanda aka ba shi N100,000 take a wurin.
Ganin haka ya yanke shawarar zuwa. Sai dai ko da aka je aka sanya wata waka wacce yaran ba su san da ita ba inda ya mike ya gwada rawar.
Yayin da yake gwadawa ne wasu suka dauki bidiyon su ka dinga yadawa a kafafen sada zumuntar zamani. A cewarsa, ya yafewa duk wanda ya yada ko ya zage shi. Amma ya tabbatar haka tashi kaddarar tazo.
Kuma ko yanzu yana nan yana fama da ciwon zuciyar wanda idan ya tashi yake neman taimako. Ya yi godiya ga Aishatul Humaira da Daddy Hikma wato Abale, wadanda yace su na matukar tallafa masa.
Anata cece-kuce akan rawan barar da mutuncin da Jarumi Tahir Fagge ya yi a wani gidan rawa da wata budurwa
Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Tahir Fagge wanda ya fi bayyana a matsayin uba a fina-finai yana shan caccaka bayan wani bidiyonsa yana tikar rawa tare da wata budurwa ya bazu a kafafen sada zumunta.
Bidiyon nasa ya janyo mutane suna ta maganganu marasa kyau akan masa’antar har wasu suna ganin bai dace dattijo irinshi ya yi irin wannan rawar ba, Masarauta Entertainment ta Youtube ta ruwaito.
Bidiyon ya ja wasu suna ganin babu wani abin fadakarwa a masana’antar Kannywood in baya ga lalata tarbiyyar jama’a.
A bidiyon ko da gani a gidan gala ne dattijon ya kwashi rawa tare da wata budurwa wacce a shekaru ya haife ta inda rawa ya kai shi har da faduwa kasa.
An ga inda ya hau kan wata waka yana wani rawa wanda matashi ne ya dace ya yi wanda har mutane suka nuna rashin jin dadinsu.
Akwai wadanda ke ganin ya kamata dattijo mai shekaru irin Tahir Fagge ya kama kansa don yanzu haka gangara ta kai.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com