31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Ƴan bindiga sun sake kai wani sabon hari, sun halaka wani ɗan kasuwa da sace mutane da dama a Katsina

LabaraiƳan bindiga sun sake kai wani sabon hari, sun halaka wani ɗan kasuwa da sace mutane da dama a Katsina

Ƴan bindiga sun sake kai wani sabon hari a ƙauyen Bakiyawa na ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina.

Harin ya auku ne a ranar Laraba inda ƴan bindigan suka halaka wani ɗan kasuwa mai sayar da hatsi mai suna Tukur Makeri, sannan kuma suka sace wasu mutanen da dama a ƙauyen.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan bindigan kuma sun raunata wasu mutum huɗu yayin da suka riƙa shiga gidaje da satar kayayyaki a shaguna a harin da ya kwashe tsawon sa’o’i uku.

Yadda harin ya auku

A cewar mani mazaunin ƙauyen mai suna Marwan Zayanna, ƴan bindigan sun dira a ƙauyen ne a kan babura sama da arba’in, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan ya sanya mutane suka ranta ana kare suna neman mafaka.

Marwan ya kuma ƙara bayyana cewa huɗu daga cikin mutanen da suka samu raunika yanzu haka ana duba lafiyar su a asibitin koyarwa na Katsina.

Ƴan bindigan suna da yawa. Da wahala na iya adadin yawan su. Sun sace mutane da yawa a ƙauyen mu bayan sun halaka Tukur Makeri, wani dillalin kayan hatsi wanda akayi jana’izar sa yau (Alhamis). A cewar Marwan

Hukumar ƴan sanda ba tace komai ba akan harin

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, rundunar ƴan sandan jihar Katsina ba ta fitar da sanarwa dangane da harin ba. Amma majiyoyin sun tabbatar da cewa jami’an ƴan sanda sun ziyarci ƙauyen sannan sun duba wuraren da harin ya ritsa da su.

Ƴan sanda sun cafke matashi mai safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar Neja

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wani mai safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar Neja.

Ƴan sanda a jihar Neja sun cafke wani matashi Umar Shehu, mai shekara 31 a duniya bisa laifin safarar makamai ga ƴan bindiga da ƴan ta’adda a jihohin Neja, Kaduna da Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ambato kakakin hukumar, Wasiu Abiodun, a cikin wata sanarwa na cewa, Shehu wanda ɗan asalin Bakori ne a jihar Katsina, an cafke shine a kwanar Dikko cikin ƙaramar hukumar Gurara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com


Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe