Francis Van-Lare ya bayyana kalubalen da ya fuskanta a aurensa na baya da ya mutu. Ya bada labari dalla-dalla inda yake shawartar mutane da su kula kwarai wurin zaben aboki ko abokiyar rayuwa, LIB ta ruwaito.
Francis ya ce ya fada soyayya mai zurfi ne tun lokacin yana karatu a fannin shari’a amma mutane su ka dinga shawartarsa da ya auri macen da ta kai shekaru 40 kuma mai yara saboda sai sun fi daidaitawa.
Ya ce ya bar budurwarsa inda aka shawarceta da ta auri yaro matashi wanda za su taso tare. Bayan daukar shawarar ne ya auri mata mai yara 4.
Ana yin auren ta dinga yada hotunansu a kafafen sada zumunta wanda hakan ya ci karo da yarjejeniyarsu wacce su ka ce kada su yada komai ga jama’a.
Ya ce bayan shekaru biyu da auren, matar da yaranta su ka taru su ka lakada masa bakin duka. Ganin haka yasa yayi gaggawar sakinta.
Ya bayyana yadda itama tsohuwar budurwarsa da aka shawarar ta auri matashi bayan kammala karatu aurenta ya mutu.
Ya bayar da labarin ne don ya sanar da jama’a cewa ba daga auren mai kananun shekaru ko kuma mai shekaru dayawa bane ke sa aure yayi karko. Hasali ma fahimtar juna da jajircewa ne sinadarin aure.
Duk da dai bai bayyana sunan tsohuwar matar tasa ba, amma a yadda ya labarta aka gane cewa Amara Blessing Nwosu, fitacciyar mai bada shawarwari akan aure da soyayya ce.
Francis da Amara sun yi aure ne a shekarar 2014 sannan sun rabu a shekarar 2017 bayan shekaru biyu da watanni kadan tarewa. Francis Van-Laare ya yi aure sau 5 kuma duk ya rabu da matansa.
Saboda ba ni da kudi, sirikata ta hana matata dawowa gidana, Magidanci gaban kotu
Wani dan kasuwa mai suna Isma’il Ibrahim ya maka sirikarsa, Zainab Muhammad a wata kotun musulunci da ke Rigasa a Kaduna bisa zarginta da hana matarsa komawa gidansa, LIB ta ruwaito.
Mai karar wanda mazaunin layin da ofishin ‘yan sanda da ke Rigasa ne, ya sanar da kotu yadda sirikarsa ta dakatar da matarsa daga komawa gidansa saboda ba ya da kudi.
A cewarsa:
Sai dai sirikar tashi ta bayyanawa kotu cewa ta hana diyarta komawa gidan mijinta ne saboda rashin kular da mijin yake nuna mata.
A cewarta, an yi wa diyarta aiki ne sannan jaririyar ta rasu. Sai dai mijin ya kasa biyan kudin asibiti inda ya bar matar a gidan iyayenta na tsawon watanni uku ba tare da nuna kulawarsa ba.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com