27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

ASUU: Dalibai sun gudanar da zanga-zangar lumana akan hanyar Gbongan zuwa Ibadan

LabaraiASUU: Dalibai sun gudanar da zanga-zangar lumana akan hanyar Gbongan zuwa Ibadan
png 20220915 190248 0000

A yau Alhamis ne mambobin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) suka gudanar da zanga-zanga a kan babbar hanyar Gbongan zuwa Ibadan, lamarin da ya haifar da cinkoso.

Daliban sun yi tir da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi.

Sai dai zanga-zangar lumana da daliban suka yi ya haifar da cunkoson ababen hawa, lamarin da ya sa dole masu ababen hawa suka dakata.

Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, Mataimakin Shugaban NANS kan Harkokin Waje, Akinteye Afeez, ya ce zanga-zangar da aka yi a kan babbar hanyar sun yi hakan ne dan sanar da gwamnatin tarayya cewa dalibai ba sa ji dadin yajin aikin da ake yi.

Mista Afeez, wanda ya ce wannan zanga-zanga da akayi sharar fage ne inda nan gaba zasu fito fiye da haka, ya ce kungiyar za ta ci gaba da mamaye manyan hanyoyi har sai an janye yajin aikin.

“wannan, yajin aikin yana na da matukar tasiri a gare mu kuma ba ma jin dadin hakan.

“Zanga-zanga yanzu muka fara har sai an janye yajin aiki.

“Mun fara zagaye ne daga Sango-Ota, zuwa kofar karbar haraji na Ibadan, yau kuma gamu a Gbongan.

“Wannan zanga-zangar da muka yi gargadi ne, mun gaji da zama a gida kuma muna son a dauki matakin gaggawa kan yajin aikin”, in ji shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, kwamandan sashin Gbongan na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Umaru Bamaiyi, ya ce jami’an sa na nan a shirye domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa.

Mista Bamaiyi, ya ce an gudanar da zanga-zangar ne a gaban sakatariyar karamar hukumar Ayedaade, inda ya ce mutanen da ke fitowa daga titin Ibadan ba za su iya wucewa zuwa Ile-Ife ba, yayin da wadanda za su je Ibadan su ma aka tare su.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe