Wani sabon bidiyon da ya fara tashe a kafafen sada zumuntar zamani ya yi matukar tayar da kura. A bidiyon, an ga yadda Ladin Cima da Ladidi Tubless, wadanda duk dattawa ne Kannywood su ka bayyana su na kwasar rawa.
Mutane da dama sun yi mamakin ganin yadda su ka jeru su na kwasar rawar tare da wasu wanda har aka dinga tsegunguma.
Kamar yadda aka saba gani, matasan kannywood kamar Maryam Yahaya, Minal Ahmad, Momi Gombe da sauransu ne ake gani su na irin wannan rawar.
Amma a wannan karon abin ya sha bamban, su Ladi da ake gani da mutunci kuma ake da ran idan sun ga yara su na irin wannan rawar za su kwaba musu ne aka ga su na kamantawa.
Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Zaynab Dalhat ce ta wallafa bidiyon inda tayi masa take da “Sun yi abin ya sha musu kai”.
Nan da nan jama’a su ka dinga zuwa karkashin bidiyon su na tsokaci. Wasu su na ganin ai ba komai bane kasancewar dama masana’antar ta yi kaurin suna wurin karancin tarbiyya.
Wasu kuma su na ganin duk da hakan, ba daidai bane dattawa da ake gani da daraja irinsu su na irin wannan rawar ta barar da daraja ba.
LabarunHausa ta tsinto wasu daga cikin tsokacin da ke karkashin bidiyon:
Ummul Jidda Busu tace:
“Allah yasa karshenmu tayi kyau.”
Malam Hussaini Ibraheem Kwari yace:
“Allah yasa mu gama lafiya.”
Bashar Tsalha yace:
“Kaico baiwar Allah.”
Muktar Adam yace:
“Allah wadaran naka ya lalace.”
Kamata yayi muje gida mu bawa Ladin Cima shawara ba wai cin mutuncin ta a shafukan sadarwa ba – Tijjani Asase
Fitaccen jarumi Tijjani Asase ya yi wani bidiyo wanda ya yi nasiha ga wadanda suka yi wallafa suna maganganu ga Ladin Cima a kafafen sada zumunta.
Hakan ya biyo bayan cece-kucen da ke ta aukuwa tun bayan an yi hira da Ladin Cima inda tace ba a biyanta kudade masu kauri ko da ta yi aiki.
Manyan darektoci irin Ali Nuhu, Falalu A. Dorayi da sauran su sun fito suna ta maganganu suna musanta ta, lamarin da Tijjani Asase ya ce bai dace ba.
Kamar yadda shafin Kannywood Media ta wallafa bidiyon sa inda ya fara da sallama tare da gabatar da kan sa sannan yace:
“Ina so in yi magana akan masu ba Ladin Cima shawara a kan social media, ya kamata ne ka kira ta gida ka yi mata magana ba ka zo kana maganganu ba.
“Meyasa zaki ce ba a baki kudi kike bata wa masana’anta suna? Ya zama shawara tsakanin ku ba wai a zo kan social media a yi mata wannan caa din. Ba daidai bane.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com