
Hukumar tsaro ta kasa, NSC, ta bayyana cewa irin yadda hukumomin tsaro ke kokari za ta kawo karshen rashin tsaro nan da watan Disambar wannan shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a yau Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron NSC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Mista Aregbesola ya kuma sanar da rusa kwamitin yaki da safarar makamai da alburusai da kuma lalata bututun mai, NATFORCE.
A cewar Mista Aregbesola, hukumar ta NSC ta gamsu da yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci, yana mai bayyana fatan ganin an kawo karshen matsalolin tsaro nan da watan Disambar wannan shekara.
Ya ce: “Majalisar ta kammala taro a yau,ta samu bayanai daga dukkan shuwagabannin tsaro kuma majalisar ta gamsu sosai da yadda dukkan shuwagabannin tsaron suke gudanar da ayyukan sui; sojoji da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro. Muna farin ciki da ayyukansu da nasarorin da ake samu ya zuwa yanzu.
“Muna kan gaba zuwa matakin karfafa duk wadannan nasarorin, nan da watan Disamba, kamar yadda shugaban majalisa,da kuma shugaban kasa suka umarta, wanda suka bayyana wa yan Najeriya haka a baya, cewar za a yi kokarin gaske wajen kalubalentar yan fashi musamman,masu tayar da kayar baya, masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da sauran laifuffuka .
“Hakazalika, mun jin dadin yadda ‘yan sandan Najeriya suka gudanar da zabukan jihar Anambra, Ekiti da Osun, wanda zaben ya nuna irin jajircewarmu ga dimokuradiyya da kuma bayyana ra’ayoyin jama’a a rumfunan zabe.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com