34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Bidiyo: Yadda asirin wata mabaraciya mai amfani da jaririn ƙarya ya tonu

LabaraiBidiyo: Yadda asirin wata mabaraciya mai amfani da jaririn ƙarya ya tonu

Asirin wata mabaraciya ya tonu inda aka gano cewa tana amfani da jaririn ƙarya wurin yin bara domin mutane su taimaka mata da sadaka.

An dai ɗauki bidiyon mabaraciyar riƙe da jaririn na ƙarya a kan wani titi a birnin Ikko wato Legas.

A bidiyon da aka yada a yanar gizo, an nuna lokacin da mabaraciyar ta tunkaro wasu fasinjoji a wata motar gida tana roƙon su da su taimaka mata riƙe da jariri a hannun ta. Shafin LIB ya rahoto.

Nan da nan fasinjojin suka zargi cewa jaririn na ƙarya ne inda suka buƙaci da ta nuna musu fuskar sa.

Mabaraciyar bata son nuna fuskar jaririn

Mabaraciyar ta ƙi yarda da ta nuna musu fuskar jaririn inda su kuma suka haƙiƙance cewa lallai sai sun ga fuskar jaririn kafin su bata kuɗi.

Ana cikin haka kawai sai mabaraciyar ta janye lullubin da aka yiwa jaririn inda ta nuna cewa ba abinda yake ciki kawai sai tarin tsummokara.

Ga bidiyon nan ƙasa:

Yawaitar barace-barace na ƙara cigaba da yaɗuwa a ƙasar nan musamman a manyan birane inda akafi samun abin sadaka.

Wasu mabaratan dai rashin yadda za suyi ne yasa suka tsunduma cikin harkar bara, bisa halin lallura ko kuma matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi.

Sai dai ba kowa ne mabaraci bane na gaskiya domin kuwa wasu lafiyar su ƙalau inda suka mayar da harkar ta bara sana’a wacce suke ci suna sha da ita.

Kudin da zan aurar da ‘ya ta nake tarawa, cewar Hadiza Ibrahim, mabaraciyar da aka kama da kudi har N500k

A wani labarin na daban kuma wata mabaraciya da aka cafke da maƙudan kuɗaɗe race kuɗin auren ƴarta take tarawa.

Sakatariyar cigaban al’umma (SDS) ta hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta samu nasarar cafke wata mabaraciya mai suna Hadiza Ibrahim ‘yar shekaru 48 da haihuwa a duniya da kudi kimanin N500,000 da kuma dala ɗari ($100).

Malam Sani Amar daraktan kula da jin dadin jama’a na sakatariyar ne ya tabbatar da kamen a ranar Talata a garin Abuja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe