27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Sarki Charles III ya karanci Al-Qur’ani mai girma

LabaraiSarki Charles III ya karanci Al-Qur'ani mai girma

Sanar da mutuwar sarauniya Elizabeth II, sarki Charles III, ɗan ta na farko ya zama sabon sarkin masarautar Ingila.

Sai dai tun naɗin sa kan sarautar, sarki Charles III ya zama abin magana a wurin mutane. Daga ƙarshe an bayyana wani muhimmin abu dangane da sarkin. Duk da cewa kirista, sarki Charles III, yana da ra’ayi mai kyau akan addinin musulunci.

Robert Jobson, shine ya bayyana hakan a littafin sa mai suna “Charles At Seventy: Thoughts, Hopes, and Dreams”. Jobson ya kuma yi nuni da cewa sarkin ya karanci littafin Al-Qur’ani mai girma. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Sarki Charles III na da fahimta mai kyau akan musulunci

A wani jawabin sa a cibiyar karatun addinin musulunci ta Oxford a 2010, sarki Charles III ya faɗi ra’ayin sa kan matsalar muhalli da sauyin yanayi bisa ilmin da yake da shi na musulunci da Al-Qur’ani.

Ya bayyana cewa musulunci ya koya masa cewa akwai iyaka na yalwatuwar albarkatun ƙasa, sannan idan ya fahimci Al-Qur’ani daidai an hana musulmai lalata su.

Ya ƙara da cewa musulunci ya koyar da cewa mu rayu da juna tare da sauran halittun dake duniyar nan, sannan yin watsi da hakan na nufin mun saɓa kan wannan tsarin na halitta.

A wata ziyara da sarki Charles III yakai jami’ar Al-Azhar dake birnin Alƙhahira na ƙasar Masar a shekarar 2006, yayi suka kan hoton zanen ɓatanci kan Annabi (SAW) da wani ɗan ƙasar Denmark yayi. Sannan yayi kira kan mutane da su mutunta addinin juna.

Wata baturiya ta musulunta bayan ta karanta Al-Qur’ani

A wani labarin na daban kuma, wata baturiya ta musulunta bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma. Afarko bata fahimci addinin musulunci da kyau ba, amma ra’ayin ta ya sauya bayan ta karanta Al-Qur’ani.

Bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma sau huɗu a wata ɗaya, wata mata mai suna Maryum  a birnin Plymouth wacce ta taso cikin addinin kirista ta musulunta. 

Wannan matakin da ta ɗauka na musulunta ya ƙada hantar ƴan’uwanta da abokai, inda har kakar ta ke bayyana musuluntar ta a matsayin ta wani ɗan lokaci ce.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe