Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar People’s Democratic Party, (PDP), Atiku Abubakar, ya bayar da sharuɗdan yin murabus ɗin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Iyorchia Ayu.
Atiku Abubakar ya bayyana sharuɗdan ne a ranar Laraba a yayin wani taro da ƙusoshin jam’iyyar na yankin Kudu maso Yamma a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Atiku ya bayyana hakan ne a yayin martanin da ya bayar kan buƙatar yankin na ganin cewa dole sai Ayu yayi murabus. Jaridar Vanguard ta rahoto.
Atiku Abubakar ya bayyana sharuɗɗan da za a bi wurin sauke Ayu
Atiku yace dole ne murabus ɗin Ayu ya kasance bisa tsarin dokoki da kundin mulkin jam’iyyar.
Atiku yace:
Ba zamu iya yin wani abu ba saɓanin abinda kundin tsarin mulkin jam’iyyar mu ya tanadar idan ba garambawul akai masa ba. Ba zamu iya wani abu ba har sai an gyara dokokin.
Dole Ayu ya tafi a bisa tsarin kundin mulkin mu da dokokin mu, idan ba haka ba, ba zamu iya samar da shugabancin da ƴan Najeriya ke buƙata ba.
Abu ne mai yiwuwa, zai iya tabbata, mun taɓa yi a baya sannan yanzu mun fara sake gudanar da hakan.
Yayi wani muhimmin kira ga ƴaƴan jam’iyyar PDP
Atiku, ya kuma roƙi ƴaƴan jami’iyyar PDP da kada su bari rikicin jam’iyyar ya sanya suyi kasa a guiwa wurin ganin jam’iyyar ta lashe zaɓukan 2023.
Tunda farko dai gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gayawa Atiku matsayar yankin kan cewa dole sai Ayu yayi murabus domin tabbatar da adalci da daidaito a jam’iyyar.
2023: Karon farko Atiku da Wike za su sulhunta
A wani labarin na daban kuma, Wike da Atiku Abubakar za su sulhunta a karon farko.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun amince da kawo karshen sabanin dake tsakaninsu.
Sun cimma matsaya
Sun cimma wannan matsaya ne a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Abuja a gidan tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Jerry Gana.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com