
Shugaban wanda ya kasance ya sami takun-saka tsakanin sa da hukumar kan yadda tsari ya tanada wajen daukar aikin yan sanda a Najeriya, ya yi murabus ne bisa dalilin rashin lafiya.
Babbar kwamishina ta biyu a hukumar ta PSC, babbar Alkali a kotun koli, Clara Ogunbiyi, wacce ke wakiltar bangaren shari’a ita ce ta karbi rikon kwaryar shugabar hukumar.
Lokacin da jaridar Vanguard ta tuntubi Kakakin Hukumar, Ikechukwu Ani kan ci gaban, ya tabbatar da murabus din amma ya bayyana cewa za a fitar da sanarwar a hukumance daga hukumar da ke bayar da cikakkun bayanai a Gobe Alhamis.
A baya an sami rahoton cewa an samu rashin jituwa tsakanin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman, da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda kan daukar ‘yan sanda aiki a wannan shekara ta 2022 wanda za a dauki kimanin ‘yan sanda 10,000.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wani dan kasar China bisa laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba
Hukumar yaki da cin hanci shiyyar garin Ilorin, EFCC, ta kama wani dan kasar China mai suna Gang Deng.
Gang dan kimanin 29 da haihuwa, an kama sa ne bisa zargin hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Ilorin, jihar Kwara.
An kama Mista Deng ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba, inda aka same shi da mallakar danyen ma’adinai ba tare da izini ba.
An kama mota dauke da ma’adanai da ake zargin lepidolite ne.
Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com