27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Dalilin da ya sa muka fi son kayan gwanjo- Cewar mazauna garin Abuja

LabaraiDalilin da ya sa muka fi son kayan gwanjo- Cewar mazauna garin Abuja
Pic.13. Goza market in Abuja 1541x1080 1

Wasu mazauna babban birnin tarayya (FCT), sun bayyana cewa sun fi son kayan sawa na gwanjo da aka fi sani da, “okrika’ saboda sun fi araha.

Mazauna garin a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ta yi da su a ranar Laraba, sun ce sun gwammace su sayi kayan gwanjo saboda sun fi jure wahala.

Grace Ike, wata mazauniyar Nyanyan, ta ce tana siya wa ‘ya’yanta tufafi da takalman gwanjo saboda suna da arha, dadewa wanda har yan baya ma zasu saka.

Ms Ike ta kara da cewa ta fi so ta yi siyayyan ta da sassafe don ta samu masu kyau kuma masu inganci.

“Dole ne mutum ya zo da wuri lokacin da za a bude dila,in ba haka ba ba za ka samu masu kyau ba,” in ji ta.

Kadijat Idris,itama mssoyiyar siyan kayan gwanjo kuma daliba dake zaune a Karu ta bayyana cewa sabbin tufafin suna da tsada sosa ba za ta iya siya ba.

A matsayina na ɗaliba,ina da kashe kuɗi da yawa don haka na gwammace in je in siya kayan sawa na gwanjo.” in ji ta.

Ta ce wasu sabbin tufafin ba sa jure wahala ; suna lalacewa da wuri musamman jeans yayin da kayan sawa na gwanjo sun fi kyau kuma suna daɗewa.
Malama kadijat ta ce galibin kayan sawa da ake samu a shagunan sayar da kayayyaki na musamman ne kuma ana sayar da su a kan farashi mai rahusa.

Ta ce maimakon ta yi amfani da kudin wajen samun sabbin tufafi, ta gwammace ta siyo abinci ita da yan uwanta.

Ms kadijat ta ce “babu bukatar siyan sabbin tufafi tunda gwanjo basuda tsada suna da araha”.

Kadijat Idris, ma’aikaciyar banki, ta ce tana sayen jakunkuna da takalma da sauran kayan kwalliya na gwanjo saboda ingancinsu, da kuma jure wahala.

Yan kasuwa

Mama Ebuka, ‘yar kasuwa ce a kasuwar Utako, ta ce ta kan sayar da kayan sawa a ranakun kasuwa a cikin babban birni da kewaye.

Ina da kwastomomi da yawa, don haka na kan je kasuwannin Mararaba duk ranar Laraba, Madalla a ranar Alhamis da kuma Garki ranar Juma’a in sayar da kayayyaki na,” inji ta.

“Ba kawai talakawa ne ke siyan kayanmu ba; Ina da kwastomomi masu kudi da yawa, waɗanda nake zaɓa musu irin kayan da suke so, ”in ji ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe