31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Cin amana: Yadda wata budurwa ta halaka kanta bayan saurayinta ya auri wata da kuɗinta

LabaraiCin amana: Yadda wata budurwa ta halaka kanta bayan saurayinta ya auri wata da kuɗinta

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Olaitan Adonis, ta halaka kanta bayan masoyinta mai suna Saheed, yayi amfani da kuɗaɗenta ya auri wata.

Budurwar ta sha wani sinadari mai guba wanda yayi sanadiyyar mutuwarta bayan ta samu raunika.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa budurwar ta haifi yaro mai shekara bakwai a duniya tare da saurayin nata.

Olaitan tana kuma ajiye kuɗaɗenta a asusun ajiyar banki na Saheed, kuma suna tare da shi a ranar 8 ga watan Satumba.

Budurwar bata san cewa zai auri wat ba

A ranar Juma’a 9 ga watan Satumba, wata ƙawarta ta sanar mata da cewa Saheed wanda suka kwana tare kafin ranar, zai angwance a ranar Lahadi 11 ga watan Satumba. Hakan ya tunzura ta matuƙa inda ta yanke shawarar kashe kanta.

A wani bayanin da shugaban inda take aiki ya fitar, yace Saheed ya samu labarin mutuwarta amma sai ya kada baki yace wannan ba abinda ya shafe shi bane.

Mai tsare min shago tasha bashi kuɗi daga shago na domin kula da shi, amma duk ya lalata gabaɗaya kuɗin. Ko ranar Juma’a sai da ta tura masa dubu goma. Bayan ta kashe kanta, mun kira shi amma sai yace wannan ba matsalar sa bace.

Tuni har makarantar da ta gama karatu suka aike da rubutun jimamin mutuwarta a shafin su na Facebook a ranar 12 ga watan Satumba. Sun kuma shawarci mutane da kada su kuskura su halaka kan su akan wani.

An kai ruwa rana yayin ceto budurwa daga hannun mai safarar mata zuwa Saudiyya kwadago

An kai ruwa rana a filin jirgin Jomo Kenyatta bayan wata mata ‘yar kasar Kenya ta dinga turjewa tana fizgar hannunta yayin da wani mai safarar mata zuwa Saudi Arabia yake yunkurin tilasta ta tafiya, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Yayin tattaunawa da ‘yan uwanta, ta bayyana musu yadda ta sha dakyar sakamakon azabtarwar da aka yi mata yayin da take kwadago a Dubai.

Haka zalika, ta bayyana wa manema labarai irin wahalar da take sha yayin neman kudi a kasar wajen.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe