37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda ango ya fasa auren amarya bayan ta ki sanar da shi wanda ya siya mata IPhone 13 Pro Max

LabaraiYadda ango ya fasa auren amarya bayan ta ki sanar da shi wanda ya siya mata IPhone 13 Pro Max

Wani matashi ya fasa auren budurwarsa bayan ta ki fada masa wanda ya siya mata waya kirar IPhone 13 Pro Max kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Dama an sa ranar aurensu ne kuma su na ta shirye-shirye, kwastam rannan tazo gida da waya IPhone 13 Pro Max.

Nan da nan masoyin nata ya bukaci sanin wanda ya siya mata wayar inda ta sanar da shi cewa dan uwanta ne.

Da ya ci gaba da bincike inda ya nemi sanin sunansa sai ta ki fadi wanda hakan yasa matashin ya fusata ya fasa auren.

An samu bayanin ne bayan abokin ango mai amfani da suna @Rita_Amy ya labarta yadda lamarin ya auku.

Tsokacin jama’a karkashin wallafar

Nan da nan mutane su ka dinga tsokaci daban-daban karkashin wallafar.

iamayotomii yace:

“Yana gudun shiga tashin hankali nan gaba kenan. Abu ne mai sauki ki fada masa wanda ya siya miki. Gara a fasa aure akan a ayi aure yazo ya lalace.

yahayajubril yace:

“Ya yi gudun shiga wani bala’in nan gaba ta hanyar dakatar da auren.”

usern92II4x9f3 tace:

Ya yi gaggawa. Dama ya bari sai ranar daurin auren sannan yaki zuwa.”

parye23 tace:

“Ya yi abinda ya dace ta hanyar fasa auren saboda gudun nan gaba yayi kuka.”

maryiyoha tace:

“Ya kamata ta iya fadin sunan dan uwantan da ya bata kyautar wayar.”

cryrilleolings tace:

Ya duba irin bala’in da zai iya shiga nan gaba ne a auren saboda yadda budurwar taki sanar da shi wanda ya siya mata IPhone 13 din.”

Yadda kawayen amarya su ka jibgi budurwar ango yayin da taje da ciki don ta hargitsa auren

Wani bidiyo ya bayyana budurwar wani ango wacce ta je ta hargitsa auren saurayinta ana tsaka da shagulgula, LIB ta ruwaito.

Mutumin, Anthony ya yi tunanin kirkirar sabuwar rayuwa tare da wata matar daban, wanda ana tsaka da daurin aurensu budurwarsa ta je ta fasa kwai ana a bainar jama’a.

Matar ta tambayi mutumin akan dalilinsa na share ta yayin da ya ke yin kamar bai gane ta ba. Sai dai yayin da take tsaka da ta da hankalin jama’a kawayen amarya su ka fara daukar matakin da su ke ganin ya dace.

A wurin ne kawayen amaryar su ka bukaci ta bar wurin don gudun ta tayar da tarzomar da hankula za su tashi. Sai dai abin mamakin shi ne yadda amarya ta nuna halin ko in kula dangane da matar ta ci gaba da tsayuwa don a daura musu aure.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe