Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa tayi abin a zo a gani duk da ƙarancin kuɗaɗen da ta samu.
Shugaba Buhari wanda yayi wannan furucin a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin jihar Imo a Owerri, babban birnin jihar, bayan ya ƙaddamar hanyar Owerri-Orlu, kashin farko na hanyar Owerri-Okigwe da kuma sake ginin majalisar jihar, wanda gwamnatin gwamnan jihar Hope Uzodinma, tayi. Jaridar The Punch ta rahoto.
Shugaba Buhari ya yaba da nasarorin da gwamnatinsa ta samu
Yace gwamnatin sa ta samu nasarari da dama duk kuwa da ƙarancin kuɗaɗen da take da su.
Wannan gwamnatin tayi matuƙar ƙoƙari sosai. Dole na faɗi hakan domin waɗanda yakamata su faɗa ba sa yi. Bansan meyasa hakan ba.
A cewar Buhari
Ya yabawa gwamnatin sa bisa fatattakar ƴan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas da kuma magance matsalar rashin ababan amfani a ƙasa wanda yace ya gaje su ne a wurin jam’iyyar PDP a 2015
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Uzodinma bisa gayyatar da yayi a karo na biyu cikin shekara ɗaya domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin sa ta gudanar.
Zai cigaba da goyon bayan jihohi
Yayi alƙawarin cigaba da goyon bayan jihohi ba tare da la’akari da bambancin siyasa dake tsakanin su domin samar da ababen morewa ga al’umma.
A cewar sa, gwamnatin tarayya zata ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar Imo domin tabbatar da cewa ta cigaba da samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar ta.
Wannan goyon bayan yana daidai wa daidai ga jihohin ƙasar nan ba tare da la’akari da bambancin siyasar dake a tsakani ba.
Buhari ya bada tabbaci.
Duk da yanayin yadda abubuwa suka chanza, tattalin arzikin Najeriya na ci gaba da bunkasa – Buhari
A wani labarin na daban kuma shugaba Buhari yace tattalin arziƙin Najeriya ba cigaba da bunƙasa duk kuwa da sauyin da aka samu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk da tabarbarewar tattalin arzikin duniya da matsalolin cikin gida, tattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da hauhawa da kuma samun cigaba.
Shugaban ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan tattalin arzikin kasa, ranar Juma’a a Abuja.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com