32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Kano: Yadda masu zub da shara su ka hada makwabta fada har su ka kusa ba hammata iska

LabaraiKano: Yadda masu zub da shara su ka hada makwabta fada har su ka kusa ba hammata iska

Masu sana’ar zubar da shara a garin Kano sun fito da sabon salon ha’inci wanda sanadin shi su ke ta hada rikici marar karewa tsakanin makwabta.

A ranar Talata, 13 ga watan Satumban 2022, wakilin Labarun Hausa ya zo giftawa Janbulo, Kabuga Estate da ke cikin Jihar Kano inda ya tarar ana ta dauki babu dadi tsakanin makwabta. Hakan ya janyo hankalinsa wanda ya nemi jin ba’asi.

bola
Masu zub da shara sun samo sabon salon ha’inci, su na ta hada jama’a rikici da makwabtansu

Anan ne ake shaida masa cewa duk makwabtan biyu sun dade su na zargin junayensu da zuba shara a harabar gidajensu, ashe ba haka abin yake ba.

Da ya tsananta tambaya ne su ka bayyana masa yadda masu zubar da shara su ka dade su na ha’intarsu.

Da zarar sun yi sallama don neman ko akwai shara, idan aka ba su sharar don su zubar tare da N100, dayake a amalanke yanzu suke zuba ta, sai su yi sallama makwabta.

Idan sun ji shiru babu alamar motsi, sai su zubar da sharar da su ka debo a gidan farko su yi gaba.

Da haka su ke tara kudi marar misaltuwa yayin da suke yin aiki kalilan. Don haka ya kamata jama’a su kula, kuma su sanya ido kwarai idan an kwashi shara a gidajensu, su dinga tabbatar da cewa an bar anguwar da ita don zub da ta inda ya dace.

Budurwa da aka dauka aikin shara da wanke-wanke tayi awon gaba gwala-gwalai na N14m, sati daya da fara aiki

Wata ‘yar aikin gida wacce da Blessing kadai aka santa, tayi layar zana, bayan zargin da ake yi mata na satar kudi da gwala-gwalai, wadanda kimarsu zata kai kimanin Naira miliyan goma sha uku da dubu dari tara (N13.9m), daga gidan uwar gidanta da take yiwa aiki, wanda yake a Victoria Island a jihar Legas.

Uwar gidan Blessing din Pearl Ogbulu, a ranar Talata 18 ga watan Janairu, tace wadda ake zargin ta aikata laifin ne, mako guda kacal da fara yi mata aiki.

Tace ta shiga wasan buya da yarinyar ‘yar asalin jihar Cross-rivers dinne tun bayan faruwar lamarin.

Jaridar PUNCH Metro, sun hada rahoton cewa, Joshua Amaha, shine ya kawo Blessing din gidan Ogbulu, wadda bata gida, a ranar da yar aikin ta ziyarci gidanta domin tattaunawa da ita.

Ogbulun ta kara da cewa, iyayen ta, wadanda tare suke zaune dasu a gidan nata, su suka shiga da Blessing din cikin gidan. A yayin tattaunawar ne sai Ogbulun tace wa yar aikin, tana da jarrabawa da zatayi da kuma wasu cike-cike a wani ofishin ‘yan sanda. Domin shirye-shirye ma sunyi nisa. A Wannan lokacin ne yarinyar yar shekara 25 tayi amfani da lokacin da bana nan ta samu damar yi min sata.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe