Kamar yadda jami’an tsaron Saudiyya su ka bayyana, sun kama wani mutum wanda yaje Makka musamman don yayi umara saboda Sarauniya Elizabeth II, The Islamic Information ta ruwaito.
Kamar yadda rahotanni su ka nuna, mutumin dan Yemen ne kuma ya saki bidiyonsa a ranar Litinin a babban masallacin Makka na Ka’aba wanda aka haramta wa wadanda ba musulmai ba zuwa.
A bidiyon, ya rike wata takarda wacce aka rubuta:
“Mu na fatan Ubangiji ya amincewa Sarauniya Elizabeth II shiga Aljanna, ya kuma sanyata cikin amintattunsa.”
Bidiyon ya yadu a shafukan ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani da ke Saudiyya, inda mutane da dama su ka bukaci a kama shi.
A Saudiyya, an haramta rike wasu tambura ko takardu a wurin ibada da ke dauke da hoto ko sunan wani.
Sannan ba a yarda ayi umara ko hajji ga wadanda ba musulmai ba kamar sarauniyar. Hakan ya biyo bayan yadda sarauniyar ke shugabantar babbar cocin Ingila ta Anglican.
Yau da safe an samu bayani akan yadda jami’an tsaro a babban masallacin su ka kama dan Yemen din da aka gani rike takardar yana sadaukar da umararsa ga sarauniyar.
Saboda abinda yayi ne aka kama shi kuma tuni an gurfanar da shi don daukar matakin da yayi daidai da abinda yayi.
Wani Likita a kasar Saudiyya ya gana da wasu tagwaye da ya raba shekaru 13 da suka gabata
‘Yan biyun lokacin da aka haife su an haife su ne a manne da juna a kasar Saudiyya. Yawancin gabobin jikinsu kamar su hanji da mafitsara suna hade ne wuri daya.
Abdallah Al-Rabiah, babban mai kula da Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sarki Salman (KSrelief), ya gana da Hassan da Mahmoud a ranar Laraba wadanda a da sassan jikin su yake a hade. ‘Yan asalin kasar Masar ne, amma mazauna birnin Riyadh, kimanin shekaru 13 kenan bayan da aka yi nasarar raba su a wani aikin tiyata da aka yi musu a garin Riyadh.
Likitoci a asibitin King Abdulaziz Medical City sun yi wa tagwayen tiyata a shekarar 2009 a lokacin da suke da watanni 9 kacal. An hade su a cikin ciki kuma an raba wasu gabobin jiki da sassan jiki, ciki har da hanji da kuma fitsari.
Al-Rabiah ya ce masarautar za ta ci gaba da zama fitila ga mabukata da marasa galihu a duk fadin duniya. Shirin likitancin da aka raba Hassan da Mahmoud, wani karin girma ne na ayyukan jin kai na kasar, in ji wanda ake gudanarwa a karkashin umarnin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman na kasar Saudiyya.
Tagwayen dai sun samu rakiyar iyayensu ne a ziyarar da suka kai babban birnin kasar Saudiyya, inda suka gode wa jama’a da gwamnatin kasar Saudiyya bisa shirya yi wa ‘ya’yansu tiyata. Lafiyar yaran ya inganta a tsawon shekaru, in ji su.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com