Wani jarumin finafinai, Ernest Obi ya bayar da wata shawara a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumban 2022 yayin da ya ke tsokaci dangane da matar da ta da aka yi garkuwa da mijinta saboda ba ya gamsar da ita a gado, Nigerian Pulse ta ruwaito.
“In har dagaske ne hujjar da ta bayar, ina bin bayanta. Ya kamata a garkame duk namijin da ya gaza gamsar da diyar mutane a daki yayi watanni uku,” kamar yadda ya wallafa.
“Shiyasa matata ke kiransa…Aikin miji… gaskiya ban san inda ta sami sunan nan ba…Amma na yarda da wannan sunan,” daga nan ya kwashe da dariya.
Sai dai a cewar jarumin, bai amince da batun garkuwa da wani ba ta ko wacce hanya. Amma maganar gaskiya ba daidai bane namiji ya kasa gamsar da matarsa.
Idan ba a manta ba, matar mai suna Joy ta ce akwai dalilin da ya sanya tayi garkuwa da mijinta, Ebong, dan asalin yankin Ntak Obio Akoa na karamar hukumar Oruk Anam.
Ta bayyana yadda bayan rashin gamsar da ita a shimfida da mijinta yake yi, ba ya kawo musu abinci.
Ta ci gaba da cewa:
“Ina yin ‘yan kananun ayyuka don in tallafawa yaranmu. Don haka ne na kitsa yin garkuwa da mijina don in samu kudin yin hidindimu.”
“Sai dai ban sami kudin fansar ba duk da na yi garkuwa da shi,” a cewarta.
Joy ta ambaci wani Udo Moji, wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar da tasa su yi garkuwa da mijinta.
Matar aure ta ɗauko hayar sa-ɗaka da zata riƙa gamsar da mijinta, ta sanya mata albashi mai
Wata matar aure mai shekaru 44 mai suna Pattheema, ta ɗauki hayar sa-ɗaka domin taimaka mata wurin gamsar da mijinta saboda ita ta kasa gamsar da shi.
Bidiyon ta na neman sa-ɗakar ya tada ƙura
Shafin Yabaleftonline ya tattaro cewa Patteema ta jawo cece-kuce a yanar gizo bayan taje TikTok inda ta tallata wannan baƙon aikin na neman sa-ɗaka guda uku domin gamsar da mijinta.
Matar auren ta bayyana sharuɗɗan aikin
A cikin bidiyon da ta fitar, tace duk masu sha’awar aikin dole ne su kasance masu shekaru 30 zuwa 35, sannan sun kammala karatun kwaleji ko digiri.
Dole ne kuma an gwada matan domin duba lafiyar su ta yadda ba su ɗauke da cutar ƙanjamau ko wasu cututtukan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com