Wata dattijuwa mai shekaru 65 ta bayyana gaban kotu inda take cigiyar angonta wanda matashi ne mai shekaru 25 yayin da take da shekaru 65, Dala Fm ta ruwaito.
Kamar yadda ta sanar da kotu, ko kazar amarci da sauran kayan makulashe bai bata ba, bata san dalilinsa na yin hakan ba, bayan auratayya ta shiga tsakaninsu ya gudu.
Yayin da alkali ya sanar da ita cewa kotu ba wurin cigaba bane, dattijuwar ta bukaci a raba aurensu tunda da kanshi ya gudu ya bar ta.
A cewarta, soyayya ce mai zurfi ta kullu tsakaninsu, wanda bayan dukkansu sun amince da juna su ka yarda har manya su ka shiga maganarsu.
ta ci gaba da cewa, lamarin da yafi daure mata kai shi ne sauya ra’ayinsa bayan sun tare.
Maimakon ya ci gaba da nuna mata soyayya da kulawa, sai ya koma akasin haka. Bayan kankanin lokaci yaa yanke shawarar guduwa daga garin duk da dai bata san dalilin wannan mataki nasa ba.
Ta zargi angon da aurenta saboda ya kula tana da abubuwan duniya. Amma bata san dalilinsa na sauya ra’ayinsa dangane da ita ba.
Tuni kotu ta amshi kukanta. Ana sa ran nan ba da jimawa ba za a datse igiyar auren nasu.
Har yanzu bata kare min ba: Tsohuwa ta dauki wankan kece raini yayin cikarta shekaru 90
Wata ‘yar kwalisar tsohuwa ta dauki wankan kece rainin yayin bikin zagayowar ranar haihuwarta kamar yadda wata ma’abociyar amfani Facebook, Zainab Ishaq ta wallafa.
Da alamu ko da ta cika shekaru 90 bata zub da makamanta na gayu ba don an ga yadda ta cakare tamkar wata karamar yarinya mai karancin shekaru.
A hotunanta an ga yadda take sanya kananun kaya masu bayyana kyakkyawar surarta duk da kasancewar jikinta duk ya yi yaushi amma bata hakura.
Tabbas hotunan sun dauki hankulan mutane da dama sakamakon yadda ta cakare, abin gunin ban sha’awa inda mutane da dama su ka dinga tsokaci a karkashin wallafar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com