Ana zargin wata jaruma a masana’antar Kannywood da gartsawa wani yaro mai suna Aliyu, mai shekaru 11 cizo bayyan ta lallasa shi.
Kamar yadda bayanai daga bakin yaron da mahaifiyarsa su ka nuna, lamarin ya faru ne a anguwar Badawa da ke cikin Jihar Kano.
Yaron ya shaida wa Dala FM cewa tsegumi aka kai wa jarumar cewa ya kira ta da karuwa, wanda hakan ya hassala ta ta bukaci ya zo shi kuma yaki zuwa.
Da alamu hakan ya yi matukar bata mata rai daga nan ta kamo hanya ta nufi har inda yake ta dinga gaura masa mari har sau bakwai.
Bayan an yi yunkurin raba su ta fusata ta samu gadon bayansa ta gannara masa cizo.
Mahaifiyar yaron ta bayyana cewa jarumar ta fito a matsayin ‘yar sanda a fim din Sirrin Boye.
Sannan ta bukaci a bi musu hakkinsu. Da alamu marin ya yi matukar ratsa yaron don wanda ya tattauna da shi ya duba yadda idon yaron ya sauya kala tare da ganin yadda cizon ya ratsa bayan yaron.
Bayan watanni 2, auren jarumar Kannywood da ta zagi Sheikh Daurawa ya mutu
Auren Jaruma Nafisat Ishak, wacce ta fito a shirin Izzar so mai dogon zamani bayan yin aure babu dadewa ya mutu kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta tabbatar.
Sai dai bata shahara ba sai bayan ta yi wata magana ta rashi ladabi ga Sheikh Daurawa, wanda ana tsaka da batun sai aka ji ta yi aure.
Sai dai bayan kasa da watanni biyu da auren kuma sai ga ta an ga ta dawo dandalin TikTok ta ci gaba da raye-rayenta har tana cewa maza ne ba sa iya rike matan shiyasa aure ke mutuwa.
Kuma kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo da ta saki a TikTok, ta ce maza ba sa rike matansu dakyau, ba sa kashe musu kudi kamar yadda su ka saba a waje.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com