32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Bidiyon TikTok din wani dattijo yana karkada labbansa ta salo na musamman ya nishadantar

LabaraiBidiyon TikTok din wani dattijo yana karkada labbansa ta salo na musamman ya nishadantar

Wani sabon shigar TikTok ya dauki hankalin mutane da dama yayin da ya saki bidiyonsa na farko wanda mutane da dama su ka nishadantu dashi a ranar 9 ga watan Satumban 2022. Nan da nan mutane su ka dinga kallo, Legit.ng ta ruwaito.

A shafin TikTok din dattijon, an ga bidiyoyi uku kacal, amma bidiyonsa na farko ya fi daukar hankalin jama’a.

An ga yadda ya kwalmada labbansa na sama da kasa a wani yanayi mai nishadantarwa tamkar yana cin yaji.

Nan da nan mutane su ka bazama su na kallon bidiyon wanda akalla yanzu haka mutane fiye da 1500 sun gani.

Tsokacin jama’a karkashin bidiyon

Tsokacin mutane daban-daban wadanda su ka yi karkashin bidiyon:

Wata Sophie sophy tace:

Bidiyo daya ya saki amma har mutanen kasashen waje sun san da shi.

akua mawuli yace:

“Ina kasa ina kwasar dariya. Na zaci shawara zai bai mu ne.”

San Davi yace:

“Yadda ya zauna hankali kwance kila zatonsa bai daura bidiyon ba.”

George Ofosuhene yace:

Shiyasa na dena hawa TikTok da dare, ta ya za ayi in yi bacci yanzu.

Wani user3390040882140 yace:

Na natsu ina kallonsa, zato na shawara zai bayar.

Wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci ta faɗa komar ƴan sanda

Ƴan sanda a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan sun cafke wata budurwa mai amfani da manhajar TikTok bisa laifin tiƙar rawa a masallaci.

An kama budurwar ne tare da ƴan tawagarta a ranar Litinin bayan bidiyonta tana rawa a masallacin Faisal ya ƙaraɗe shafukan sada zumunta. Jaridar Islamic Information ta rahoto.

Limamin masallacin ya kai ƙorafi akan budurwar

Limamin masallacin Mohsin Ishaq shine ya shigar da ƙorafi akan budurwar da ƴan tawagarta a ciki har da mai ɗaukar bidiyon, a ofishin ƴan sanda na Margalla bisa tanadin dokar PPC 295-A.

A cikin ƙorafin na sa ya bayyana cewa yaga wani bidiyo a shafukan sada zumunta na wata budurwa ba sanye da kallabi ba kuma cikin shiga mara kamala. Kwatsam kawai sai ta shiga cikin harabar masallacin na Faisal inda ta keta rigar mutuncin wurin ibadar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe