23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

An kai ruwa rana yayin ceto budurwa daga hannun mai safarar mata zuwa Saudiyya kwadago

LabaraiAn kai ruwa rana yayin ceto budurwa daga hannun mai safarar mata zuwa Saudiyya kwadago

An kai ruwa rana a filin jirgin Jomo Kenyatta bayan wata mata ‘yar kasar Kenya ta dinga turjewa tana fizgar hannunta yayin da wani mai safarar mata zuwa Saudi Arabia yake yunkurin tilasta ta tafiya, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Yayin tattaunawa da ‘yan uwanta, ta bayyana musu yadda ta sha dakyar sakamakon azabtarwar da aka yi mata yayin da take kwadago a Dubai.

Haka zalika, ta bayyana wa manema labarai irin wahalar da take sha yayin neman kudi a kasar wajen.

Da farko dai an ga yadda ta fuskanci mai safarar matan a fusace yayin da ‘yan uwanta ke kokarin dakatar da ita daga isa wurinsa.

Yayin da ta kai wurinsa inda ta dinga zazzaga masa masifa, ta yi barazanar ci masa mutunci tare da tabbatar da sai ya biyata duk wahalhalun da ta sha a Dubai da kuma kudaden da ‘yan uwanta su ka kashe don ceto ta.

“Kan me za ka zo nan wurina? Ya dace ace kana can kana taimakon mutane ne! Dole ne ka biya ‘yan uwana duk kudin da su ka kashe kafin su dawo da ni,” a cewar matar wacce take magana cike da bacin rai.

Yayin da yayi yunkurin fizgarta, matar ta fadi a kasa, amma duk da haka sai da ya finciketa. Ganin yadda mutane su ka taru a wurin ne yasa mutumin ya tsere don gudun jama’a su far masa.

Wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci ta faɗa komar ƴan sanda

Ƴan sanda a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan sun cafke wata budurwa mai amfani da manhajar TikTok bisa laifin tiƙar rawa a masallaci.

An kama budurwar ne tare da ƴan tawagarta a ranar Litinin bayan bidiyonta tana rawa a masallacin Faisal ya ƙaraɗe shafukan sada zumunta. Jaridar Islamic Information ta rahoto.

Limamin masallacin ya kai ƙorafi akan budurwar

Limamin masallacin Mohsin Ishaq shine ya shigar da ƙorafi akan budurwar da ƴan tawagarta a ciki har da mai ɗaukar bidiyon, a ofishin ƴan sanda na Margalla bisa tanadin dokar PPC 295-A.

A cikin ƙorafin na sa ya bayyana cewa yaga wani bidiyo a shafukan sada zumunta na wata budurwa ba sanye da kallabi ba kuma cikin shiga mara kamala. Kwatsam kawai sai ta shiga cikin harabar masallacin na Faisal inda ta keta rigar mutuncin wurin ibadar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe