29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyar ASUU kotu

LabaraiYajin aiki: Gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyar ASUU kotu

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, yace gwamnatin tarayya ta yanke shawarar maka ƙungiyar malaman jami’a (ASUU) kotu saboda tattaunawar da ɓangarorin biyu ke yi ta tarwatse.

Lamarin zuwa kotun na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin albashi ga malaman na jami’a sannan tayi alƙawarin sanya N150bn a cikin kasafin kuɗin 2023 a matsayin kuɗin farfaɗo da jami’o’in tarayya, wanda za a fitar da kuɗaɗen ga jami’o’in a farkon watanni uku na shekarar.

An buƙaci kotun da ta saurari ƙarar cikin gaggawa

A wata wasiƙa da Ngige, ya aikewa babban rajistaran kotun ma’aikata ta Najeriya, a ranar 8 ga watan Satumba, ya nemi kotun da ta saurari ƙarar cikin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar yajin aikin.

Jaridar Daily Trust ta samu ganin wasiƙar wacce kotun ta amsa ranar 9 ga watan Satumba, mai taken “miƙa lamarin sa’insar da ke tsakanin gwamnatin tarayya/ministirin ilmi da ƙungiyar malaman jami’a (ASUU)”.

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa, ”Duba da cewa ƙungiyar ASUU suna ta yajin aiki tun 14 ga watan Fabrairu, kuma sun ƙi janye yajin aikin, zan so a ce an saurari wannan matsalar cikin gaggawa domin a kawo ƙarshen ta”.

Ministan ya haƙiƙance cewa wasiƙar ta sa tayi daidai da bisa damar da yake da ita wacce doka ta bashi.

ASUU: Yajin aiki ya mayar da wani dalibin karatun likitanci zama mai sayar da abinci a jihar sokoto

A wani labarin na daban kuma, yajin aikin ASUU ya sanya wani ɗalibin likitanci zama mai sayar da abinci a jihar Sokoto. Ɗalibin yana karatu a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto.

Tsawaita yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi ya mayar da Usman Abubakar-Rimi, dalibin karatun likitanci a jami’ar Usman Danfodiyo ta Sokoto (UDUS) dan kasuwa.

Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a yau Juma’a a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya zama mai sayar da abinci don rayuwa mai inganci a dalilin yajin aiki da malaman jami’o’in gwamnati ke yi wanda hakan sanya dalibai zama a gida.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe