27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wani dan kasar China bisa laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

LabaraiHukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wani dan kasar China bisa laifin hakar ma'adanai ba bisa ka’ida ba
IMG 9723

Hukumar yaki da cin hanci shiyyar garin Ilorin, EFCC, ta kama wani dan kasar China mai suna Gang Deng.
Gang dan kimanin 29 da haihuwa, an kama sa ne bisa zargin hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Ilorin, jihar Kwara.

An kama Mista Deng ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba, inda aka same shi da mallakar danyen ma’adinai ba tare da izini ba.

An kama mota dauke da ma’adanai da ake zargin lepidolite ne.

Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Yadda muke sa ido kan mutanen da ke cire kudi a bankuna, muna yi musu fashi -Cewar Wanda ake zargi

Wani mai satar kudin mutane da ‘yan sanda suka kama a jihar Zamfara ya bayyana yadda yake yi wa mutane fashi bayan sun cire kudi a bankuna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya yi ikirarin cewa wanda ake zargin, Umar Usman mai shekaru 39 a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shi mamba ne na wata kungiyar da ta kware wajen sa ido kan kwastomomin da ke fitar da kudi a bankuna da wasu cibiyoyin hada-hadar kudi, sai shi kuma ya bisu ya yi musu fashi.

Wanda ake zargin ya amsa cewa shi da wasu ’yan kungiyar suna gudanar da ayyukansu a jihohin Borno, Bauchi,Kebbi da kuma Sakkwato.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, hadin kan da wanda ake zargin ya bayar shi ne ya sanya aka kwato N3,500,000 mallakar wani Nura Shinkafi, ma’aikacin ofishin saka hannun jari na jihar Zamfara, Gusau.
Wanda abun ya rutsa da shi ya bayyana yadda wasu da ba a san ko su waye ba suka fasa gilashin gefen hagu na motarsa kirar Peugeot 406 inda suka yi awon gaba da jakarsa dauke da bakar HP Laptop dinsa mai lamba CND0515RPN, wanda kudinta zai kai N250,000, katin I.D na jihar Zamfara guda daya da kudinsa N3,500,000.

Rundunar ‘yan sandan ta ce yayin da ta samu nasarar cafke Mista Usman, har yanzu ana ci gaba da kokarin cafke wani da ake zargi,mai suna Abdul Sun, wanda mazaunin garin Zariya ne a jihar Kaduna.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya umurci jama’a musamman masu yin hada-hadar kudi a bankuna da kuma duk wata cibiya da su kula da wannan kungiya tare da tabbatar da sun kai rahoton duk wani mutum da suke zargi ga ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe