37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Dalilin da ya sa shirin Fim din ‘Izzar So’ ya karbuwa sosai –Cewar Lawal Ahmad

LabaraiKannywoodDalilin da ya sa shirin Fim din ‘Izzar So’ ya karbuwa sosai –Cewar Lawal Ahmad
Lawal Ahmad Izzar So

Wannan shirin ‘Izzar So’ na masana’antar Kannywood mai taken soyayya, a halin yanzu shi ne fim din Hausa da aka fi kallo a yanar gizo.

Ya yadu a tashar YouTube kuma ya kewaya gidaje a arewacin Najeriya da ma wajenta.

An shirya shi a tashar YouTube ta Bakori TV, wanda ke ɗaukar mabiya sama da 953,000.

An yi kiyasin cewa, a awa ashirin da hudu kashi daya na iya samun ‘yan kallo 400,000

An bayyana cewa shirin yanzu yakai, kashi na 98 a YouTube.

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma , Ahmad Lawan ne ya shirya kuma ya ba da umarni.

Fitattun jaruman Kannywood Ali Nuhu, Ahamd Lawan, Aisha Najamu da Nana Izzar So sune suka takao a cikin shirin.

Mista Lawan, a wata hira da PREMIUM TIMES ta yi da shi ya ce shirin ‘Izzar So’ ya ginu ne a kan koyarwar Musulunci da kuma tafarkin Annabi Muhammad (SAW).

“Fim din, Izzar So, nasara ce a gare ni. Ina tsammanin wannan babban abu ne domin yana da asali game da yadda musulmi na gaskiya ya kamata ya kasance a rayuwa da kuma rayuwarsa ta soyayya. Fim ne da ya sa mutane da yawa suka sake chanza tsarin rayuwar su.

“Mun shirya wannan shiri ne domin mu nunawa mutane yadda za su yi rayuwarsu kan tafarkin mai kyau da kuma yadda Annabi (SAW) ya koyar da mu. Mutane da yawa sun jinjina min akan wannan fim din.

“Sannan ina alfahari a dalilin shirin, ‘Izzar So; mutane biyu sun shiga musulunci. Mata biyu sun sun fito ne daga Gombe inda suka nuna min su masoyan fim din ne kuma suna ganin ya kamata su zama Musulmai. Sun ce sun koyi abubuwa da yawa game da addinin Musulunci a fim din kuma suna son su zama Musulmi. Yanzu su Musulmai ne.”

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe