29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Dubai na shirye-shiryen gina katafaren wurin shaƙatawa wanda babu irin sa a duniya

LabaraiDubai na shirye-shiryen gina katafaren wurin shaƙatawa wanda babu irin sa a duniya

Indai ana maganar samar da wuraren shaƙatawa masu matuƙar ƙayatarwa ne to ƙasar haɗaɗɗiyar daular Larabawa, Dubai, na a sahun gaba a duniya.

Dubai tayi suna matuƙa gaya wurin samar da wuraren shaƙatawa masu ɗaukar hankalin ƴan yawon buɗe ido daga sassa daban-daban.

Duk a kowace shekara ƙasar na samun ɗumbin baƙi ƴan yawon buɗe ido daga ƙasashen duniya daban-daban.

Domin cigaba da ɗaukar hankali da janyo masu yawon buɗe ido cigaba da yin tururuwa zuwa ƙasar, a yanzu haka shirye-shirye sun kankama na gina wani sabon katafaren wurin shaƙatawa a ƙasar wanda babu irin sa a duniya.

Yadda wurin zai kasance

Katafaren sabon wurin shaƙatawar da za a gina a ƙasar zai kasance da sabon salo wanda ba a taɓa ganin irin sa ba a duniya.

Wurin shaƙatarwa za a yi masa siffar wata, kuma zai lamushe maƙudan kuɗaɗe. Shafin Africa Updates ya rahoto.

Wani kamfanin gine-gine na ƙasar Kanada zai gudanar da aikin wanda aka ƙiyasta zai cinye kuɗi kimanin dala biliyan biyar ($5bn).

Kamfanin mai suna Moon World Resort Inc na shirye-shiryen gina wurin shaƙatarwa wanda zai yi tsawon kafa 735 a Dubai, sannan za a iya kammala aikin cikin watanni arba’in da takwas kacal.

Idan aka kammala aikin na wurin shaƙatawar, ana tsammanin samun baƙi ƴan yawon buɗe ido sama da mutum miliyan biyu da dubu ɗari biyar (2.5m) a shekara. Za a samar da wurin hutawa da wurin raƙashewa.

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen gina sabon birni wanda zai yi gogayya da Dubai

A wani labarin na daban kuma gwamnatin Najeriya na shirin gina wani katafaren birni wanda zai yi gogayya da Dubai.

Gwamnatin Tarayya da manhajar cryptocurrency Binance Holdings Ltd sun fara tattaunawa dangane da yadda za su gina wani katafaren wuri na bunkasa tattalin arziki musamman don taimaka wa masu sana’o’i don su inganta su da fasahar zamani, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda Hukumar Nigerian Processing Zone ta bayyana a wata takarda, hadin guiwar ta su zai samar da wata cibiya ne mai kama da ta kasar Dubai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe