27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Nafi Buhari ƙaunar Najeriya nesa ba kusa ba -Sheikh Ahmed Gumi

LabaraiNafi Buhari ƙaunar Najeriya nesa ba kusa ba -Sheikh Ahmed Gumi

Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari baya ƙaunar ƙasar nan kamar yadda yake yi.

Sheikh Ahmed Gumi ya faɗi hakan ne yayin da yake martani kan kamun da hukumar DSS tayi wa Tukur Mamu.

A wa’azin sa na sati da yake gabatarwa a masallacin Sultan Bello, Kaduna, Gumi yace yakamata gwamnati ta nemi afuwa bisa cin zarafin Mamu. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Sheikh Ahmed Gumi na son ganin an samu zaman lafiya

Yace shi da kan sa ya ɗauki aniyar ganin ya sanya ƴan bindiga sun sassauta abubuwan da suke yi domin samun ɗorewar zaman lafiya, amma waɗansu mutanen ba su son gaskiya.

A matsayin mu na mutane, ba zamu kasa taɓuka komai ba. Na san harkokin tsaron nan saboda nima a baya ina daga ciki. Don haka nasan yadda suke aikin su sannan nasan munafurcin su. Ko Sardauna bai tsira daga tuggun su ba, haka Murtala, Maimalari da IBB har da Buharin shi kan sa. Dukkan su sun sha wahalar tuggun su.

Cikin kwana-kwanan nan Malam Goni ya faɗa wa tuggun su; lokacin da wasu matasan sojoji suka kashe shi. Waye yake alfahari da su?

Na yanke shawarar saka baki cikin wannan lamarin domin taimakawa a samu zaman lafiya a ƙasa. Bari na gaya muku ko shugaban ƙasa bai ƙaunar ƙasar nan kamar yadda nake yi saboda bani da wata ƙasa idan ba Najeriya ba.

Ina son ƙasar nan ta samu zaman lafiya, hakan ya sanya na sanya rayuwata cikin hatsari na shiga daji domin samo hanyar magance matsalar tsaro. Amma wasu mutanen basa son hakan ya faru.

Akwai mutanen da basu son a samu zaman lafiya a Najeriya

Ba su son samuN hanyar da za a magance matsalar domin sun fahimci cewa da gaske nake, sai suka yanke shawarar fara ɓata min suna, su na haɗa ni da ta’addanci.

Abinda ya basu haushi shine lokacin da nace mutanen nan sun cancanci su samu ababen more rayuwa kamar su asibiti, makarantu kamar dai yadda akayi wa tsagerun Neja Delta. Hakan ya sanya suka fara zage-zage.

Sojoji zasu iya fata-fata da maboyar ‘yan bindiga cikin minti 15 amma hakan bazai yi amfani ba, matsalar siyasa ce ba ta karfin makamai ba – Inji Sheikh Ahmed Gumi

A wani labarin na daban kuma, Sheikh Ahmed Gumi yace sojoji za su iya gamawa da ƴan bindiga amma hakan bai da amfani.

A wata hirar hadakar ‘yan jarida da cibiyar bincike da rahoton kwakwaf (ICIR) ta gabatar tare da shehin malamin nan Ahmad Gumi, malamin ya fadi hanyoyin da za’a kawo karshen matsalar ‘yan bindiga, wadda ta tagayyara wasu bangarori na Arewa maso yammacin Najeriya

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe