23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Ƴar baiwa: Yadda wata ƙaramar yarinya ta haddace sannan ta rubuta Al-Qur’ani a Katsina

LabaraiƳar baiwa: Yadda wata ƙaramar yarinya ta haddace sannan ta rubuta Al-Qur'ani a Katsina

Wata ƙaramar yarinya mai shekara 13 a duniya, Zuwaira Ahmed, a ƙauyen Kagara na ƙaramar hukumar Kafur a jihar Katsina, ta haddace sannan ta rubuta Al-Qur’ani mai girma hizifi sittin da hannu.

Da yake magana a wurin walimar da aka shirya domin ƙarrama yarinyar a ranar Asabar, hakimin Mahuta, Alhaji Bello Abdulkadir, ya nuna farin cikin sa akan wannan gagarumin cigaban da aka samu.

Yayi bayanin cewa wannan gagarumar nasara ce da aka samu a ƙauyen, da jihar gabaɗaya musamman a fannin ilmin addinin musulunci. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Abdulkadir ya kuma yabawa iyayen yara na yankin, malamai da sauran jagororin al’umma bisa tabbatar da cewa yaran su sun taso cikin tarbiyya mai inganci inda ya nemi da su cigaba akan wannan turbar.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Kafur, Alhaji Garba Abdullahi-Kanya, ya yaba sosai da abinda yarinyar tayi inda ya bada tabbacin goyon bayan karatun ta tun daga matakin sakandire har zuwa na gaba da sakandire.

Ta haddace Al-Qur’ani cikin shekara huɗu

Shugaban makarantar su yarinyar Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, yace an kafa makarantar ne domin sanya ingantaccen ilmin addinin musulunci a zukatan yara masu tasowa na ƙauyen.

A cewar sa, yarinyar ta haddace Al-Qur’ani mai girma cikin shekara hudu, sannan ya alaƙanta wannan nasarar data samu bisa goyon bayanta da iyayenta suka yi da kuma jajircewar da malamanta suka nuna.

A nasa jawabin, mahaifin yarinyar Malam Ahmed Sani ya nuna godiyar sa bisa kulawar da aka nuna masa shi da ɗiyar ta sa inda ya roƙi iyaye da su bar ƴaƴansu su rinƙa samun ilmin addini da na boko.

Wata baturiya ta musulunta bayan ta karanta Al-Qur’ani

A wani labarin na daban kuma, wata baturiya ta musulunta bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma.

Bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma sau huɗu a wata ɗaya, wata mata mai suna Maryum  a birnin Plymouth wacce ta taso cikin addinin kirista ta musulunta. 

Wannan matakin da ta ɗauka na musulunta ya ƙada hantar ƴan’uwanta da abokai, inda har kakar ta ke bayyana musuluntar ta a matsayin ta wani ɗan lokaci ce.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe