Wani limamin ɗariƙar Anglican a wata coci a Nnewi jihar Anambra, Rev. Ogbuchukwu Lotanna, yayi murabus daga muƙamin sa a cocin.
A cikin takardar murabus ɗin nasa, Lotanna, wanda kuma lauya ne, ya fito daga Mbanagu Otolo Nnewi, yace ya samu wahayi ne domin ya fara tafiyar goyon baya kan auren mata da yawa.
Jaridar The Punch ta ambato cewa yayi iƙirarin cewa wahayin da ya samu domin goyon bayan auren mata da yawa, na da kuɗirin rage zunuban zinace-zinace a cikin al’umma.
Ya gano cewa auren mace fiye da ɗaya ba laifi bane
Yayi nuni da cewa auren mata da yawa ba zunubi bane, saɓanin huɗubar da ake yi ta akasin hakan.
A cewar sa abinda ubangiji ya tsana shine saki kowane iri sannan da lalata da matar wani.
Ya kuma haƙiƙance cewa ubangiji ya fi so mazaje su auri fiye da mace ɗaya, a maimakon bin matar wani ko ƴan matan da ba auren su suka yi.
Cocin Anglican na ɓoye gaskiya game da auren mace fiye da ɗaya
Yace coci ta ɓoye wannan bayanin ga mabiyanta na tsawon lokaci sannan yanzu lokaci yayi da yakamata a gayawa mutane gaskiya.
Ya kuma ƙarfafa guiwar mazaje kan su auri ƴan matan da cin amanar matan su da su domin gujewa shiga wuta. Yayi amanna cewa abu ɗaya da yake ba daidai ba kan auren fiye da mace ɗaya shine zama a cocin da bata yarda da hakan ba.
Ya kuma bayyana cewa wannan sabuwar tafiyar tasa za a kira ta sunan “Gideonites”, yayin da kuma wurin ibadar su za a kira shi da “majami’ar Gideonites”
A bayyane yake cocuna musamman cocin Anglican sun sha yin da’awar hana auren mata da yawa, amma ubangiji ya buɗe idanuna nagane gaskiya cewa auren mata da yawa ba zunubi bane.
A cewar sa
Abokan aikin sa dai sun kaɗu matuƙa gaya kan wannan matakin da ya ɗauka, inda suka ce ba su taɓa zaton faruwar hakan ba.
Lotanna ya samu matsayin limamin ɗariƙar Anglican a 22 ga watan Disamba, 2019 a cocin Cathedral ta St. Mary’s Uruagu, a Nnewi. Yana kuma auren Chinyere Abigail, wacce ta fito daga ƙauyen Umuogbu Achara a ƙaramar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra.
Fasto ya mutu bayan ya sa an birne shi a kabari inda ya sha alwashin zai tashi irin yadda ‘Jesus’ yayi
Wani fasto a kasar Zambia ya mutu bayan ya yi yunkurin mutuwa kuma ya tashi kamar yadda Jesus yayi.
Hakan yasa yasa a daure hannayensa sannan aka birne shi a kabari na tsawon kwana uku.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com