32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Wata sabuwa: Kotun shari’ar musulunci ta bayar da umurnin cafke wasu jaruman Kannywood

LabaraiKannywoodWata sabuwa: Kotun shari'ar musulunci ta bayar da umurnin cafke wasu jaruman Kannywood

Wata kotun shari’ar musulunci ta ba ƴan sanda umurnin cafke wasu jaruman Kannywood mutum 10 bisa yin abubuwa  da ka iya gurɓata tarbiyyar matasa a shafukan sada zumunta.

Kakakin kotun, Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana cewa kotun ta bayar da umurnin ne ranar Talata data gabata bayan wasu lauyoyi sun shigar da ƙara inda suka nemi da a hukunta su bisa yin waƙoƙi da rawa kan waƙokin batsa, sannan da kuma sanya su a yanar gizo. Rahoton Channels Tv.

Ko su wanene jaruman da kotun tace a cafke

Jaruman da ake zargin sun haɗa da maza huɗu da mata shida ciki har da wani fitaccen mawaƙin gambara, fitacciyar ƴar fim da kuma sanannan mutum takwas a TikTok masu mabiya da yawa.

Babbar kotun shari’ar musulunci ta ba kwamishinan ƴan sanda umurnin cafke mutum 10 da ake zargi domin yin bincike kan rawar da suka taka wurin nuna abubuwan rashin tarbiyya.

A cewar Ibrahim

Mawaƙin gambara, Ado Gwanja, ana tuhumar sa da sakin wata waƙa mai suna “A sosa”, wacce sauran jaruman suka yi rawa a cikin ta a yanar gizo.

Waƙar da kuma bidiyoyin sun janyo cece-kuce a Kano, inda aka yi ta sukar yanayin maganganun dake cikin waƙar da kuma irin rawar da akayi.

Har yanzu ba a kama kowa ba

Sai dai Ibrahim yace ba wanda aka kama ko a ka miƙa hannun ƴan sanda daga cikin waɗanda ake zargin, kwana tara bayan an bayar da umurnin.

Za mu jira ƴan sanda su kammala binciken su kafin sanin matakin da kotu zata ɗauka na gaba.

A cewar sa

Har yanzu ba wanda daga cikin jaruman yace uffan dangane da lamarin, sannan Ado Gwanja da wasu fitattu daga cikin su, yunƙurin jin ta bakin su yaci tura.

Dalilan da yasa aka haramta waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja

A wani labarin na daban kuma, an bayyana dalilan da yasa aka haramta waƙar ‘Warr’ ta Ado Gwanja.

Gwamnatin Najeriya ta haramta waƙar nan ta ‘Warr’ ta shahararren mawaƙin nan Ado Gwanja wacce yayi a baya-bayan nan.

Sanarwar haramcin waƙar ta ‘Warr’ ya biyo ta hannun hukumar kula da kafafen sadarwa ta Najeriya, NBC. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe